Ribadu: Muhimman Abubuwa 7 Da Baku Sani Ba Game Da Sabon Mai Ba Da Shawara A Harkokin Tsaro
- Shugaba Bola Tinubu ya nada mukamai da dama tun bayan kama rantsuwar aiki a matsayin shugaban kasa
- Bola ya nada wasu mukamai ciki har da Mallam Nuhu Ribadu a matsayin mai ba da shawara a harkan tsaro
- Ribadu kafin wannan mukami, ya rike mukamai da dama da kuma gwagwarmayar siyasa
Shugaba Bola Tinubu ya nada Mallam Nuhu Ribadu a matsayin mai ba da shawara akan harkar tsaro (NSA).
Wannan nadi na zuwa kwanaki kadan bayan Tinubu ya ba shi mukamin mai ba shi shawara na musamman akan tsaro.
Legit.ng ta tattaro abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da sabon mai ba da shawara akan harkar tsaro.
1. Ranar haihuwarshi
Premium Times ta bayyana cewa an haifi Mallam Nuhu Ribadu a ranar 21 ga watan Nuwamba 1960, a Yola babban birnin jihar Adamawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Ilimi
Ribadu ya fara makarantar Firamare a Aliyu Mustapha da ke Yola a 1966, ya karbi takardar shaida a 1973.
Ya wuce makarantar sakandare ta Yelwa daga 1973 zuwa 1977, kafin ya wuce Kwalegin Fara Karatu ta CPS da ke Yola daga 1978 zuwa 1980.
Ya kammala digiri dinsa a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a 1983, daga nan ya wuce makarantar Lauyoyi da kuma samun kira daga kungiyar a 1984.
3. Farkon shugaban EFCC
Nuhu Ribadu shi ne farkon wanda ya fara rike shugabancin Hukumar Yaki da Cin Hanci ta EFCC.
Ya kasance shugaban hukumar da yafi kawo sauyi a yaki da cin hanci a kasar cikin shekaru uku.
4. Jami'in dan sanda
Ribadu ya shiga aikin dan sanda bayan kammala bautar kasa.
Ribadu ya samu karin girma zuwa mataimakin babban sifetan 'yan sanda (AIG) a watan Maris na shekarar 2007.
5. Takarar shugaban kasa a jam'iyyar ACN
Nuhu Ribadu ya tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar ACN a 2011, cewar Sahara Reporters.
6. Dan takarar gwamnan Adamawa a 2015
Ribadu ya tsaya takarar gwamnan jihar Adamawa a jam'iyyar PDP a 2015, inda ya sha kaye a wurin Jibrilla Bindow na jam'iyyar APC, Premium Times ta tattaro.
7. Lambobin yabo
Ribadu ya samu lambobin yabo da dama lokacin da yake dan sanda da kuma shugaban EFCC.
Lambar yabo ta babban sifetan'yan sanda a 1997 da 1988 da kuma 2000.
Lambar yabo daga shugaban kasa a 2015, da kuma gwarzon shekara daga gidan jaridu a 2014.
A shekarar 2010, Ribadu ya samu lambar yabon zama mai digirin digirgir a fannin shari'a a jami'ar Babcock da ke jihar Ogun.
Tinubu Ya Kara Wa Nuhu Ribadu Girma Zuwa Bai Bada Shawara Kan Tsaron Kasa
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya karawa Mallam Nuhu Ribadu matsayi zuwa mai ba da shawara akan harkokin tsaro na kasa.
“Mai Laifi Ke Tsoro Na”: Faifan Bidiyon Hirar Bawa Ya Yadu Kafin Tinubu Ya Dakatar Da Shi Daga Shugaban EFCC
Wannan na zuwa kwanaki kadan bayan shugaban ya dakatar da wasu masu mukamai da dama a kasar.
Bayan nada Mallam Nuhu Ribadu, Tinubu ya ba da wasu mukamai da dama da suka shafi tsaro.
Asali: Legit.ng