Tashin Farashin Kayayyaki: Jerin jihohin Najeriya 10 Da Suka Fi Fuskantar Matsalar A 2023
- Tun bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin mai, 'yan Najeriya ke tunanin wannan mataki zai kawo hauhawan farashin kaya
- Ba a je ko ina ba, kayayyakin masarufi suka yi tashin gwauron zabi saboda karin kudin sufuri daga mafi yawan direbobi sakamakon tsadar man fetur
- Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) a rahotonta, ta bayyana jerin johohin da suka fi fuskantar hauhawan farashin kayayyaki a kasar tun shekarar 2022
Kamar yadda wani masanin zuba hannun jari ya bayyana, za a samun tashin farashin kayayyaki a Najeriya zuwa kashi 23 saboda wasu matakai da gwamnati ke dauka.
Matakan sun hada da cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi da kuma darajar Naira da ta karye a kasuwanni.
Har ila yau, Hukumar Kididdiga ta kasa (NBC) ta ce an samu karin hauhawan farashi daga kashi 22.22 a watan Afrilu zuwa 22.41 a watan Mayu.
Jihohin Ondo da Kogi da Rivers su ne akan gaba a hauhawan farashin kayayyaki
Jihohin Ondo da Kogi da Rivers sun fuskanci hauhawan farashin kayayyaki da kashi 22.84 da 25.70 da kuma 25.02 a jere daga watan Mayu 2022 zuwa watan Mayu 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin da Taraba da Sokoto da Plateau suka fuskanci mafi karancin tashin farashin kayayyakin a cikin shekara, cewar jaridar Vanguard.
A cikin watanni, Osun da Ebonyi da Taraba sun fi samun tashin farashin kayayyaki da kashi 3.05 da 3.02 da kuma 2.81 a jere, rahoton Naira Metrics.
Jihohi 10 da suka fi samun tashin farashin kayayyaki
Legit.ng tattaro cewa jihohin Ondo da Kogi da Rivers sun fi sauran jihohi samun hauhawan farashin kayayyaki.
Yayin da Sokoto da Taraba da Kano suka fi samun karancin farashin kayayyaki tun watan Mayu na shekarar bara.
Jihar Ondo ta fuskanci tashin farashin kayayyaki fiye da kowace jiha da kashi 30.26 sai Kogi da kashi 29.52 da kashi 29.8.
Jerin jihohi 10 da suka fi kowace jiha fuskantar tashin farashin kayayyaki a watan Mayu:
1. Ondo
2. Kogi
3. Rivers
4. Bayelsa
5. Ebonyi
6. Lagos
7. Anambra
8. Oyo
9. Delta
10. Yobe
CBN Ya Kara Kudin Ruwa 'Don Dakile Hauhawan Farashin Kaya'
A wani labarin, Babban Bankin Najeriya, CBN ya kara kudin ruwa har zuwa sama da kashi 18.
Bankin ya ce ya yi hakan ne don dakile hauhawan farashin kayayyaki da mutanen kasar ke fuskanta a halin yanzu.
Tashin farashin kayayyaki a makon da ya gabata ya haura kashi 22.22 musamman kayayyakin abinci da aka fi amfani da su a gidaje.
Asali: Legit.ng