Sabon Gwamnan CBN: Tsohon Gwamna, Masu Bankuna Da Wasu Kwararru Da Ke Sa Ran Gaje Kujerar Emefiele
- Dakatar da gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele da Shugaba Bola Tinubu ya yi, ya farantawa 'yan Najeriya da dama
- Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka Tinubu da mukarrabansa na can na ta tunanin wanda zai gaji kujerar Emefiele
- Akwai jerin wadanda ake sa ran za su iya gadar kujerar Godwin Emefiele wadanda suka kasance kwararru a fannin tattalin arziki
Rahotanni sun bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu da hadimansa suna can suna ta neman wanda zai gaji kujerar gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele.
Shugaban da mukarrabansa suna duba yiwuwar duba manyan mutane masu kwarewa don basu mukamai daban-daban a sabuwar gwamnatin, cewar Legit.ng.
Rahoton ya ce kujarae gwamnan CBN ta na bukatar natsuwa don tabbatar da wanda zai gaje ta ya kawo sauyi musamman yadda tattalin arzikin kasar ya lalace.
Daga cikin wadanda ake saran za su gaji kujerar akwai:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
1. Fola Adeola
Shi ne wanda ya kasance shugaban bankin GT na farko sannan kuma ya kawo sauyi a ma'aikatar fansho ta zamani.
2. Bode Agusto
Ya kirkiri kamfanin ba da bashi na kasa kuma shi ne tsohon daraktan ofishin kasafi na Tarayya.
Ya kammala digiri dinsa a jihar Lagos a bangaren lissafin kudi.
3. Oluyemi Cardoso
Tsohon shugaban bankin Citi kuma tsohon kwamishinan ci gaban tattalin arzikin jihar Lagos a lokacin mulkin tsohon gwamna Tinubu.
4. Olawale Edun
Ya kasance tsohon kwamishinan kudi a jihar Lagos lokacin wa'adin mulkin sabon shugaban kasa, Bola Tinubu.
Ya zuwa yanzu, an ba gwamnan rikon kwarya damar ci gaba da rike mukamin CBN, kafin daga bisani s samo wanda ya fi cancanta ya gaje kujerar da Emefiele ya bari.
Idan baku manta ba, koran Emefiele ya zo da cece-kuce a kasar nan, musamman wadanda ke sukar tsohon gwamnan.
Yadda Tinubu Ya Hango Take-Taken Emefiele, Ba Zai Wanye Da Shi Lafiya Ba
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya kada su raunata ganin yadda sauya fasalin Naira ke damunsu.
Tinubu ya sha fada a baya cewa, sauya fasalin kudaden an yi ne don kawo masa cikas a zabensa.
Daga bisani Tinubu ya dakatar da Godwin Ememfiele da kuma umartar bincikarsa akan wasu korafe-korafe.
Asali: Legit.ng