Manyan Jiga-Jigan APC da Suka Fito Fili Suka Zargi Godwin Emefiele da Kitsawa Tinubu Tuggu a Zaben 2023

Manyan Jiga-Jigan APC da Suka Fito Fili Suka Zargi Godwin Emefiele da Kitsawa Tinubu Tuggu a Zaben 2023

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele a kujerar gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni, kana ya umarci mika mukamin ga mataimakin gwamnan CBN, Adebisi Sonubi.

Kafin dakatar da shi Emefiele, wasu gwamnonin jam’iyyar APC sun zargi tsohon gwamnan na CBN da yiwa jam’iyyarsu tuggu a zaben da ya gabata.

Wasu daga cikin gwamnonin sun yi Allah-wadai tare da kalubalantar sauya fasalin Naira na CBN a gaban kotu bayan kaddamar da kudin a watan Disamba.

Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, ‘yan APC sun yi zargin cewa Emefiele ya bullo da batun sauyin ne don ganin ya yiwa Tinubu tuggu ya fadi a zaben da aka yi a watan Faburairu.

Gwamnonin da suka fara hango matsala game da Emefiele
El-Rufai, Emefiele da Tinubu | Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

1. Nasiru El-Rufai

Tsohon gwamnan jihar Kaduna na daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki da ya kalubalanci Emefiele a lokacin da aka kaddamar da sauyin kudin Najeriya, wanda daga baya ya jefa kasar cikin matsalar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Emefiele: Jerin Zarge-Zargen Da Ake Yi Wa Dakataccen Gwamnan CBN Yayin da DSS Ta Yi Sabon Yunkuri

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

El-Rufai dai kafin ya garzaya kotu, ya zargi Emefiele da yin aiki tare da jam’iyyar PDP ta hanyar tsiro da dokokin da ka iya kawar da damar nasarar APC a zaben 2023.

2. Abdullahi Ganduje

Na gaba-gaba daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC da suka zargi tsohon gwamnan CBN, Emefiele da yin aiki wajen rusa jam’iyyar APC a zaben 2023 shi ne tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Ganduje ya ce manufar sake fasalin Naira da kuma dokar da Emefiele ya kawo ta kayyade adadin kudaden da za a ke cirewa a bankunaya jefa mutane da dama a jiharsa cikin yunwa da fatara.

3. Bello Matawalle

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle na daga cikin fitattun jiga-jigan jam'iyyar APC da suka yi zargin cewa manufar sauya fasalin Naira da Emefiele ya kawo ita ce ta dakile damar nasasar jam'iyyar APC a zaben 2023.

Biyo bayan kayen da ya sha a zaben gwamna da aka gudanar a jihar a ranar 18 ga watan Maris, Matawalle ya yi zargin cewa matsayarsa na kin jinin sauya fasalin Naira ne ya sa munafukan Aso Rock suka kitsa kwace kujerarsa.

Kara karanta wannan

DSS Ta Jero 'Laifuffukan' Emefiele, Za Ta Bukaci Karin Lokacin Cigaba da Tsare Shi

4. Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi mai barin gado na daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC da suka yi fatali da manufar sauya fasalin Naira da Emefiele ya kawo ana saura watanni 2 a kada kuri’u zaben shugaban kasa na 2023.

Yahaya Bello ya bi sahun El-Rufai da Matawalle wajen kalubalantar sahihancin manufar dokar kudi ta CBN, inda suka samu nasarar jikkata tasirin dokar jim kadan bayan kammala zaben shugaban kasa.

An kori Emefiele daga CBN

Yanzu dai ta kare, tunda Bola Tinubu ya bayyana dakatar da Emefiele daga ci gaba da rike ragamar gwamnan CBN.

Tinubu ya ce, dakatar da Emefiele zai ba gwamnatinsa damar ci gaba da bincike don gano inda matsalolin kudi suke a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng