Sarki Mafi Dadewa a Najeriya Ya Rasu Bayan Ya Shafe Shekaru 64 a Karagar Mulki

Sarki Mafi Dadewa a Najeriya Ya Rasu Bayan Ya Shafe Shekaru 64 a Karagar Mulki

  • Allah ya yiwa basarake mai fada a ji na masarautar Obudu rasuwa, wanda shine mahaifin daya daga ministocin Najeriya
  • Rahoton da muke samu ya bayyana tarihin dattijon mai tsawon shekaru kuma mai fada a ji a jihar Cross River
  • An kuma bayyana cewa, shine basaraken da ya fi kowa dadewa a kan karagar mulki a kasar nan, dansa ya ce mafi dadewa a Afrika

Jihar Cross River - Labarin da ke iso mu ya ce, Allah ya yiwa Joseph Davies-Agba, basaraken gargajiya na masarautar Obudu rasuwa.

Dansa Kjay Jedy-Agba ne ya sanar da mutuwar Davies-Agba a ranar Lahadi a Calabar, babban birnin jihar Cross River, TheCable ta ruwaito.

Marigayi sarkin gargajiyan, wanda ya shafe shekaru 64 a kan karagar mulki, ana bayyana shi a matsayin sarki mafi dadewa a kan karagar mulki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Aka Yi Wa Wasu Matasa Biyu Yankan Rago a Jihar Filato

Allha ya yiwa mahaifin minista rasuwa
Hoton marigayi sarki | Hoto: Kjay Jedy-Agba
Asali: Facebook

Bayanan sanar da mutuwa masu daukar hankali

A cewar sanarwar rasuwar da ta fito daga dansa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Cikin tsananin zafi a zuciya ina sanar da ku rasuwar mahaifina abin kaunata, Mai Martaba, Joseph Davies-Agba, OON, 'Uti Item III na Utugwang', Uti Ukani I na masarautar Obudu, Muhimmin Basarake a karamar hukumar Obudu kuma shugaban jami’ar jihar Cross River.
“Fara hawansa kan kujerar sarautar gargajiya ya fara ne shekaru 64 da suka gabata, wanda hakan ya sa ya zama mai yiwuwa sarkin gargajiya mafi dadewa a Afirka.
“Mu, dangi na kusa, mai yiwuwa ba mu da cikakken bayani game da yadda jana’izarsa za ta kasance idan aka yi la’akari da matsayinsa na sarki.
"Tilas ne mu bi al'adar mutanenmu a cikin dukkan al'amuran da za su wakana har su kai kai shi makwancinsa na karshe."

Jedy-Agba ya ce za a sanar da jama'a cikakkun bayanai game da jana'izar marigayi sarkin da zarar an kammala bukukuwan gargajiya.

Kara karanta wannan

Masarauta: Kwankwaso ya fadi abin da Abba Gida-Gida zai yi kan kujerar sarkin Kano Sanusi II

Hakazalika, ya nemi da a sanya su a addu'ar hakuri da kuma jure wannan babban rashin da ya same su.

Meye matsayinsa da alakarsa da tarihin Najeriya?

Ya zuwa rasuwarsa, marigayi sarkin na Obudu ya kasance shugaban jami'ar jihar Cross River (UNICROSS).

Hakazalika, shine mahaifin Goddy Jedy Agba, karamin ministan makamashi a Najeriya, rahoton Daily Trust.

Najeriya na ci gaba da rashin manyan dattawanta a shekarun baya-bayan nan, jama'a na shiga jimamin gaske.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel