Cire Tallafin Mai: Dole A Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, TUC Ta Fadi Bukatunta

Cire Tallafin Mai: Dole A Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, TUC Ta Fadi Bukatunta

  • Kungiyar Gamayyar ‘Yan Kasuwa ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya kara mafi karancin albashi zuwa N200,000
  • Kungiyar ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar wanda shugabanta da sakatarenta suka sanya wa hannu
  • Kungiyar ta ce ya kamata a kaddamar da wannan kafin karshen watan Yuni, don rage radadin cire tallafin mai

FCT, Abuja – Kungiyar Gamayyar ‘Yan Kasuwa (TUC) ta bukaci shugaban kasa, Bola Tinubu da ya kara mafi karancin albashi zuwa N200,000 don rage radadin cire tallafi.

Kungiyar ta ce ya kamata a kaddamar da hakan kafin karshen watan Yuni, yayin da ta ce dole a duba hauhawan farashin kayayyaki.

Kungiyar TUC na son FG ta kara mafi karancin albashi zuwa N200,000
TUC ta nemi FG ta kara mafi karancin albashi zuwa N200,000. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban Kungiyar, Festus Osifo da kuma babban sakatarensa, Nuhu Toro su suka bayyana haka a wata sanarwa da suka sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Bayan Ya Yi Rusau, Abba Gida Gida Zai Koma Kan Masu Satar Kaya da Sunan Ganima

Wannan na daga cikin bukatun da TUC ta mika ga gwamnati

Sun tabbatar da cewa wannan na daya daga cikin bukatun da suka mika zuwa ga Gwamnatin Tarayya yayin tattaunawarsu, cewar jaridar Daily Trust.

Osifo ya ce sun kuma bukaci a dawo da farashin litan mai na farko yayin da ake ci gaba da tattaunawar, inda ya ce gwamnonin jihohi su tabbatar da biyar mafi karancin albashin.

A cewar sanarwar:

“Ma’aikatan da suke daukar kasa da N200,000 ko $500 a ma’aikatun gwamnati ko masu zaman kansu a wata, ya kamata su samu hutun biyan haraji.
“Sannan masu daukar N200,000 zuwa N500,000 a samar musu da alawus daga litan mai don samun sauki.
“Samar da tallafi yadda gwamanti za ta biya N10 a kowane lita da ‘yan kasa za su amfana da shi, don kawo karshen matsalolin da ke harkan kiwon lafiya da ilimi."

Sanarwar ta kara da cewa:

Kara karanta wannan

Tsadar mai: Kungiyar 'yan jarida ta tubure, ta ce za ta yi gagarumar zanga-zanga a Najeriya

“Gwamnatin Tarayya kuma ya kamata ta samar da ababan hawa a kowane mataki don saukaka wa ‘yan kasa.
“Haka gwamnatocin jihohi ya kamata su rage kudin sufuri don rage radadi ga ma’aikata da kuma dalibai."

TUC ta kuma bukaci gwamnati ta samar da magani don rage radadi

Osifo har ila yau, ya bukaci gwamnati ta samar da isassun magani da zai wadatar da ‘yan Najeriya a hukumar ba da tallafin kowon lafiya ta NHIS, cewar Tribune.

Ya kara da cewa, dole gwamnati ta inganta wutar lantarki a kasa don bunkasa kamfanoni da za su samar da sauki ga ‘yan kasa.

Abubuwa 5 Da ’Yan Najeriya Ya Kamata Su Sani Game Da Cire Tallafin Mai

A wani labarin, tun bayan cire tallafin mai a Najeriya, gidajen mai da dama sun rufe tare da karin farashin litan mai.

Hakan ya sa Kungiyar NLC suka shiga tattaunawar gaggawa da Gwamnatin Tarayya don shawo kan matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.