Ba Zan Karbi Mukami a Gwamnatin Tinubu Ba, Sai da Sharadi 1, Wike Kan Mulkin Tinubu

Ba Zan Karbi Mukami a Gwamnatin Tinubu Ba, Sai da Sharadi 1, Wike Kan Mulkin Tinubu

  • Tsohon gwamna Nyeson Wike na jihar Rivers ya ce ba zai karbi wani mukami ba a gwamnatin Tinubu har sai ya tuntubi mai dakinsa
  • Wike ya ce duk da cewa Shugaba Tinubu bai masa tayin mukami ba, amma idan hakan ta faru to sai ya tuntubi 'yan uwansa
  • Ya musanta rade-radin da ke yawo cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki ta APC bayan ganawarsa da Tinubu

Jihar Rivers - Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya ce idan Shugaba Tinubu ya bashi mukami sai ya tuntubi mai dakinsa kafin ya karbi mukamin.

Wike ya bayyana cewa matarsa da 'yan uwansa sune mutanen farko da zai tuntuba kafin ya karbi mukami.

Nyesom Wike
Ba Zan Karbi Mukami a Gwamnatin Tinubu Ba, Sai da Yardan Mai Dakina, Cewar Wike. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a ganawarsa da 'yan jarida a ranar Lahadi 5 ga watan Yuni, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Shugaba Tinubu, Wike Ya Fayyace Gaskiya Kan Yuwuwar Ya Koma Jam'iyyar APC

Jigon na jam'iyyar PDP ya ce har yanzu Tinubu bai ce masa komai ba akan bashi mukami, amma har yanzu bai wuce yi wa kasarsa hidima ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya ce yana bukatar hutu bayan mulkin shekaru takwas

Ya ce yana bukatar hutu yanzu tun da ya yi mulki har na tsawon shekaru takwas.

A cewarsa:

"Zan huta yanzu, na yi mulki har na tsawon shekaru takwas, saboda haka ina bukatar hutu.
"Tinubu bai mini magana akan zai bani mukami ba, amma banyi girman da zan ki mukami ba, bai taba ce min zai bani mukami ba.
"Idan ya bukaci mu yi aiki tare, abin da zan fara yi shine zan tuntubi matata da 'yan uwa da abokan arziki in ji tunaninsu akan abin.
"Zan kuma binciki kaina in gani, idan na shirya, ba zan taba yin abin da ban shirya masa ba.

Kara karanta wannan

“Sai An Tauna Tsakuwa Idan Za a Kai Najeriya Gaba”: Wike Ya Goyi Bayan Tinubu Kan Cire Tallafin Mai

Wike ya musanta cewa zai koma jam'iyyar APC

Wike ya yi fatali da jita-jitan da ake yadawa cewa yana da shirin sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki ta APC, bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a ranar Juma'a 2 ga watan Yuni.

Ya ce ya kai wa shugaban ziyara ne kadai don ya nuna goyon bayansa kwana hudu bayan an rantsar da shi, Daily Post ta tattaro.

Bani da Shirin Sauya Sheka Daga PDP Zuwa Jam'iyar APC, Cewar Wike

A wani labarin, tsahon gwamnan jihar Rivers, Nyeson Wike ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa zai koma jam'iyyar APC.

Wike ya bayyana haka ne bayan an gano shi tare da Shugaba Tinubu suna ganawa kwana hudu da rantsar da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel