'Yan Ta'addan ISWAP 82 Sun Nutse Cikin Ruwa a Kokarin Tserewa Dakarun Sojoji

'Yan Ta'addan ISWAP 82 Sun Nutse Cikin Ruwa a Kokarin Tserewa Dakarun Sojoji

  • Ƴan ta'addan ISWAP da dama sun baƙunci lahira lokacin da suke ƙokarin guduwa daga luguden wutan dakarun sojoji
  • Ƴan ta'addan tare da iyalansu sun nutse ne a cikin ruwa a yayin da suke yunƙurin tsallakawa zuwa jamhuriyar Nijar
  • Da yawa daga cikin waɗanda suke sheƙe barzahu mata ne da ƙananan yara waɗanda ba za su iya yin iyo ba a cikin ruwan

Jihar Borno - Aƙalla mayaƙan ƙungiyar ƴan ta'addan Islamic State of West African Province(ISWAP), 82 ne tare da iyalansu suka nutse a cikin wani rafi a yankin Damasak na jihar Borno.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴan ta'addan tare da iyalan na su sun fito ne daga yankin tafkin Chadi, sun nutse ne yayin da suke ƙoƙarin tsallakawa jamhuriyar Nijar, a ƙoƙarin tserewa luguden wutan da dakarun sojoji suka kwashe kwana biyu suna yi musu a tsakanin ranakun 2 da 3 na watan Yuni.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Najeriya Sun Ziyarci Tsohon Shugaba Buhari a Daura, Hotuna Da Bayanai Sun Fito

'Yan ta'addan ISWAP 82 sun nutse a cikin kogi Borno
'Yan ta'addan na tserewa dakarun sojoji ne Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Majiyoyi masu tushe sun tabbatarwa da Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa lamarin ya auku ne daban-daban a tsakanin ƙauyukan Bulama Modori, Kaneram, Dogomolu da Jokka.

Rafin ya faro ne tun daga Komadougou a jihar Yobe, ya biyo ta tafkin Chadi sannan ya shige jamhuriyar Nijar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyoyin sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun yi ƙoƙarin tserewa ne bisa tsoron halaka a fagen daga bayan sun samu labarin cewa dakarun sojoji sun ƙaddamar da wani atisaye na musamman a yankin.

Mafi yawan waɗanda suka mutu mata ne da ƙananan yara waɗanda ba za su iya yin iyo ba, yayin da wasu kuma da dama suke jinyar wahalar da suka sha. A halin da ake ciki ana cigaba da tsamo wasu gawarwakin.

Dakarun Sojoji Sun Halaka 'Yan Ta'addan ISWAP a Jihar Borno

Kara karanta wannan

Gwara Haka: Dakarun Sojoji Sun Sheke 'Yan Bindiga Da Dama a Zamfara, Sun Ceto Mutanen Da Aka Sace

A wani labarin na daban kuma, dakarun sojojin rundunar haɗin guiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF), sun sheƙe ƴan ta'addan ISWAP a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun halaka ƴan ta'adda mutum uku na ISWAP, a wani sintiri da suka fita a yankin tafkin Chadi a jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng