Tinubu Na Yin Ganawar Farko Da Shugabannin Tsaro a Fadar Aso Rock

Tinubu Na Yin Ganawar Farko Da Shugabannin Tsaro a Fadar Aso Rock

  • A karon farko, Shugaba Bola Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro tun bayan da ya karɓi mulki a ranar Litinin
  • Janar Lucky Irabor, babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya ne ya jagoranci hafsoshin zuwa wajen taron a fadar shugaban ƙasa
  • Sufeto janar na 'yan sanda, Usman Alkali-Baba, da Yusuf Bichi, Darakta-Janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ma sun samu halartar taron

Abuja - A yanzu haka shugaban kasa Bola Tinubu na ganawarsa ta farko da shugabannin tsaro a fadar gwamnati Aso Rock da ke Abuja.

Daily Trust ta ruwaito cewa, babban hafsan tsaron ƙasa, Janar Lucky Irabor ne ya jagoranci manyan hafsoshin tsaron zuwa fadar shugaban ƙasa, a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni da muke ciki.

Shugabannin Tsaron Najeriya suna taro da Tinubu
Tinubu Na Yi Ganawar Farko Da Shugabannin Tsaro a Fadar Aso Rock. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Duka manyan hafsoshin tsaro sun halarcin taron

Shugabannin tsaron da suka halarci taron sun haɗa da babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya, babban hafsan sojojin ruwa, V. Admiral Awwal Gambo, babban hafsan sojojin sama, Air Marshal Isiaka Amao, da kuma sufeto-janar na 'yan sanda, Usman Alkali Baba.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani a Ganawar Tinubu da Kungiyar Kwadago

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran shugabannin tsaron sun kuma haɗa da darakta-janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi; da darakta-janar na hukumar leƙen asiri ta ƙasa (NIA), Ahmed Rufa'i Abubakar.

Tinubu ya gana da shugaban EFCC

A ranar Laraba da ta gabata ne, Tinubu ya gana da shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock.

An kuma wallafa batun taron a shafin Tuwita na hukumar gidan talabijin ta Najeriya (NTA), a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni.

Taron dai shi ne irinsa na farko da Tinubu ya yi da hafsoshin tsaron ƙasar da shugabannin hukumomin leƙen asiri tun bayan da ya karbi ragamar mulki daga hannun tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Abin Da Buhari Ya Gaza Yi A Shekarunsa 8 Kan Mulki, Mataimakin Shugaban APC Ya Yi Bayani

Ƙungiyar dattawan Arewa ta buƙaci Tinubu ya cika alƙawuran da ya ɗauka

Ƙungiyar dattawan Arewa ta buƙaci sabon shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya cika alƙawuran da ya ɗauka kan batun tsaro da rage raɗaɗin talauci a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Ƙungiyar ta yi wannan kira ne a cikin saƙon taya murna da ta aikewa Shugaba Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, ta hannun daraktan watsa labaranta Dakta Hakeem Baba-Ahmed.

Asali: Legit.ng

Online view pixel