"Matata Ta Cika Kyau, Tsoro Nake Wani Ya Dauke Ta" Miji Ya Nemi Kotu Ta Rabasu

"Matata Ta Cika Kyau, Tsoro Nake Wani Ya Dauke Ta" Miji Ya Nemi Kotu Ta Rabasu

  • Wani magidanci ɗan kimanin shekaru 40 a duniya ya garzaya Kotu ta raba aurensa da matarsa saboda kyaunta ya cika yawa
  • Mista Anold, ya faɗa wa Kotun cewa babu macen da ta kai matarsa kyau a faɗin garinsu, yana tsoron wasu su ja hankalinta
  • Shugaban Ƙotun, wanda ya ce bai taɓa haɗuwa da Kes irin wannan ba, ya yanke hukuncin kan lamarin

Wani magidanci ya shaida wa Kotu cewa ba ya buƙatar tarayya da matarsa, Hilda Mleya, yar kimanin shekara 30 a duniya saboda ta cika kyau.

Tribune ta tattaro cewa mutumin mai suna, Arnold Masuka, ɗan shekara 40 a duniya, ya yi wannan ikirarin ne a gaban Kotun yanki da ke garin Lusaka na kasar Zinbabwe.

Neman saki a Kotu.
"Matata Ta Cika Kyau, Tsoro Nake Wani Ya Dauke Ta" Miji Ya Nemi Kotu Ta Rabasu Hoto: dailytrust
Asali: UGC

A cewar Mista Anold, yana roƙon Kotu ta datse igiyoyin auransa da matarsa saboda tsananin kyaun da Allah ya bata, wanda ke hana shi sukuni da rashin bacci.

Kara karanta wannan

Ni Mutum Ne Mai Saurin Fushi, In Ji Gwamna Babagana Zulum

Ya ce yanayin ya yi muni har ta kai ga yana fargabar tafiya wurin aiki ya barta ita kaɗai a gida saboda tsoron wani daban ka iya zuwa ya kwace masa ita.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Arnold ya ɗauki matakin garzayawa Kotu ta raba aurensa ne saboda ya gano cewa matarsa ta fi kowace mace kyau a lungu da saƙon garin Gikwe na ƙasar Zimbabwe.

Bugu da ƙari, a bayanan da ya gabatar wa Kotu, ya ce matarsa tana da yawan murmushi a kowane lokaci kuma idan ta yi yana kara mata kyau.

Amma a cewarsa, abinda yake tsoro da ɗar-ɗar a cikin zuciyarsa, irin wannan murmushin da baya rabuwa da fuskarta ka iya jan hankalin wasu maza, su zo su raba shi da ita.

Wane hukunci Kotu ta yanke?

Alkalin Kotun, mai shari'a Chenjerai Chireya, ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da yake jagorantar shari'a makamanciyar wannan.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ɗebo da Zafi, Ya Fallasa Masu Satar Dukiyar Talakawa a Kusa da Buhari

Da yake yanke hukuncin kan batun, Mista Chireya, ya buƙaci iyayen miji da matar su sa baki, su sulhunta ma'auratan domin samun nutsuwa da zaman lafiya a tsakaninsu.

Sabon bincike kan lokacin kwanciyar jin daɗi tsakanin miji da mata

A wani labarin kuma Sabon bincike ya nuna lokacin da ya fi dacewa namiji ya kwanta da matarsa su raya Sunnah.

Wasu kwararrun masu bincike a Burtaniya sun gano lokacin da ya fi dacewa mutane su kwanta da matansu na aure domin kula da kiwon lafiyarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262