Tsohon Sojan Amurka Ya Shiga Hannu Kan Zargin Shigo da Makamai Najeriya

Tsohon Sojan Amurka Ya Shiga Hannu Kan Zargin Shigo da Makamai Najeriya

  • An gurfanar da wani dan kasar Amurka, Donn Perkins bisa zargin shigo da makamai kasar Najeriya
  • Perkins wanda tsohon sojan ruwan Amurka ne, an gurfanar da shi a gaban babbar kotun tarayya
  • An yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu a kotun tarayya da ke jihar Lagos

Jihar Lagos - Mai shari’a Abimbola Awogboro na babbar kotun tarayya da ke Lagos ta tasa keyar wani dan Amurka mai suna Donn Perkins a gidan gyaran hali na Ikoyi bisa zargin shigo da makamai Najeriya.

Perkins wanda ya ce shi tsohon sojan ruwan Amurka ne, an gurfanar da shi ne a gaban kotun wanda hukumar shige da fice na kasar ta shigar bisa zargin aikata laifuka guda hudu.

Kotu a Najeriya
Tsohon Sojan Ruwan Amurka Ya Shiga Hannu Bisa Zargin Shigo da Makamai Najeriya. Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Hukuncin wanda aka yanke a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu, an kama wanda ake zargin ne a watan Faburairu a tsibirin Tin-can a Apapa da ke jihar Lagos, cewar jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Buhari: Ba Za Mu Daina Bada Kwangiloli da Cin Bashi ba Sai Daren 29 ga Watan Mayu

Mai gabatar da kara ta fadi laifukansa

Mai gabatar da kara, Mrs Bode-Ayeni ta fadawa kotu cewar an kama dan Amurkan ne saboda ya shigo da muggan makamai ba ta hanyar da ya dace ba, cikin makaman akwai AK-47 fiye da 30 sai kuma harsasai da dama da sauran muggan makamai a tare da shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta kara da cewa wanda ake zargin ya boye makamai a cikin kwantaina da ya yi kokarin shigo da su kasar Najeriya ta tsibirin Tin-can a Lagos, ta ce hakan ya sabawa dokokin Najeriya wanda ya ke dauke hukunci mai tsanani.

Perkins ya musanta zargin da ake tuhumarsa akai

Wanda ake zargin ya musanta zargin da ake masa, a dalilin haka, mai gabatar da kara ta roki kotun da ta sake saka rana don ci gaba da sauraran karar da kuma ajiye shi a gidan yari har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

Kara karanta wannan

Wuta Ta Kona Gidan da Ganduje Zai Zauna Bayan Ya Bar Fadar Gwamnatin Kano

Yayin da lauyan wanda ake zargi, Blessing Jaiyeola ta roki korun da ta ajiye Perkins a wurin masu korafe-korafe har zuwa lokacin ci gaba da sauraran karar, cewar rahotanni.

Mai shari’a, Awogboro bayan sauraran korafe-korafe daga kowane bangare, ta umarci da a ajiye wanda ake zargin a gidan gyaran hali kuma ta dage sauraran karar har zuwa 6 ga watan Yuni don ci gaba da sauraran karar.

Amurka ta Kakaba Wa 'Yan Najeriya Takunkumin Hana Shiga Cikinta Saboda Raina Dimokradiyya

A wani labarin, hukumomi a kasar Amurka sun ce za su kakaba wa 'yan Najeriya takunkumin hana shiga kasar bisa zargin yi wa dimukradiya karan tsaye.

Sakataren gwamnatin kasar, Anthony Blinken ne ya bayyana haka a ranar 15 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel