Bidiyon Wani Mutum Yana Tuka Motarsa Mai Siffar Takalmi Ya Dauka Hankali

Bidiyon Wani Mutum Yana Tuka Motarsa Mai Siffar Takalmi Ya Dauka Hankali

  • Bidiyon wani mutumin China yana tuka katoton takalmi a China ya bar mutane baki bude a soshiyal midiya bayan ya yadu
  • Bidiyon da ke nuna mutumin yana duka motarsa mai sifar takalma ya ja hankalin mutane da dama
  • Abun ya baiwa mutane da dama mamaki, inda wasu suka yi hasashen komawa ga irin wannan mota cikin barkwanci

A kwanan nan ne wani mutumin kasar China ya fito titi cikin wata katafariyar motarsa mai siffar takalmi.

Bidiyon wanda shafin @thiennguyen030913 ya wallafa ya nuno wani mutumi yana tuka katon takalmi da tsawonsa ya kai mita uku.

Wani mutum yana tuka mota mai sifar takalmi
Bidiyon Wani Mutum Yana Tuka Motarsa Mai Siffar Takalmi Ya Dauka Hankali Hoto: Tiktok/@thiennguyen
Asali: TikTok

Cike da karfin gwiwa, mutumin da ba a san ko wanene ba ya hau titi yana tuka motarsa mai siffar takalmin dauke da wata tuta a bayansa.

Abun ya kayatar sosai lokacin da mutumin ya yi fakin katafaren takalminsa a wani wuri da aka tanada don fakin motoci.

Kara karanta wannan

Matar Aure ta Sha Suka Bayan Ta Boye Fuskar Mijinta a Hotunan Shakatawa Da Suka Fita

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu wucewa da mutanen da ke wajen sun gaza hakuri inda suka tsaya cirko-cirko suna kallon ikon Allah, yayin da suka ware idanunsu cike da al'ajabi da mamaki.

Bidiyon ya yadu inda mutaned suka bayyana ra'ayoyinsu da kuma yin yan rubuce-rubuce da Zai dace da bidiyon.

Zuwa yanzu bidiyon ya tara 'likes' miliyan 1 da martanoni a TikTok.

Jama'a sun yi martani

@ffy2x6 ya ce:

"Gobe, za ka fara tuka safa."

@castedsmart ya ce:

"Ina daya kafar? na tuka na bi ka a baya."

@chrispanayi8 ya ce:

"Shin motarka fata ce ko roba?"

@brinahjackie5 ya ce:

"Na gaza daina yin dariya."

@decemberprince17 ya ce:

"Yi tunani da ace dukka motoci su sauya zuwa takalma a titi."

@glorymelvine ta ce:

"Ba abun da ba za a iya yi ba a China, China yi mun guda biyu."

Kara karanta wannan

“Allah Ya Amsa Addu’arta”: Yar Najeriya Ta Samu Miji Tana Da Shekaru 53, Ta Yi Wuff Da Angonta Mazaunin Turai a Bidiyo

Kalli bidiyon a kasa:

Yadda budurwa ta mallaki motar miliyan 36 da sana'ar gwanjo

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa ta garzaya dandalin soshiyal midiya don baje kolin tsadaddiyar motar naira miliyan 36 da ta gwangwaje kanta da shi.

Matashiyar wacce ta ce bata bukatar namiji ya dauke mata dawainiyarta na yau da kullun ta ce sana'ar gwanjo ta ke yi kuma a cikin haka ne ta siya motar tata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel