Labari Mai Dadi: Jirgin Saman Najeriya Zai Iso a ranar Juma’a, In Ji Ministan Buhari

Labari Mai Dadi: Jirgin Saman Najeriya Zai Iso a ranar Juma’a, In Ji Ministan Buhari

  • Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya bayyana lokacin da jiragen saman Najeriya za su iso kasar
  • Sirika ya ce jiragen za su iso a ranar Juma'a, 26 ga watan Mayu domin fara aiki da jigilar kayayyaki
  • A cewarsa za a kaddamar da jirgin a kalolin Najeriya don cika alkawaran da gwamnati ta dauka a ma'aikatar sufurin jiragen sama
  • Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta kammala wa'adinta a ranar 29 ga watan Mayu

Jirgin saman Najeriya zai iso kasar a ranar Juma'a, Juma'a, 26 ga watan Mayu gabannin fara aiki, kamar yadda ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya tabbatar.

A wata hira da ya yi da gidan Talbijin na Channels, minsitan ya bayyan cewa jirgin saman Najeriya zai isa kasar a cikin kwanaki biyu daga cikin tsare-tsaren da ake yi na fara aikinsa da kuma fara jigilar kayayyaki.

Kara karanta wannan

Minista Ya Cigaba da Korar Shugabannin Hukumomi, Ya Ce Babu Sani ko Sabo a Mulki

Jirgin saman Najeriya
Labari Mai Dadi: Jirgin Saman Najeriya Zai Iso a ranar Juma’a, In Ji Ministan Buhari Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Facebook

Ya yi alkawarin cewa za a kaddamar da jirgin a kalolin Najeriya domin cika dukka alkawaran da gwamnatin ta dauka a ma'aikatar sufurin jiragen sama.

Sai dai kuma, ya bayyana cewa abu daya tilo da bai kammalu ba shine wajen saukar jirgin, wanda ke a filin jirgin sama kuma an kammala kaso 60 cikin 100 na wajen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, an kammala aikin ginin filin jirgin, kuma ana sa ran gwamnatin gaba za ta kammala aiki a kan filin jirgin.

Jirgin saman Najeriya zai fara aiki kafin 29 ga watan Mayu, Sirika

Sirika ya bayyana a taron kungiyar masu ruwa da tsaki na ma'aikatar sufurin jiragen sama da aka yi a Abuja a watan Maris cewa jirgin saman Najeriya zai fara aiki kafin karshen gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Dubu ta Cika: Sojoji Sun Kwamushe Rikakken Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanan Sirri a Arewa

Ministan ya kuma bayyana cewa kaso 98 cikin 100 na aikin ya kammala.

Da yake amsa wata tambaya kan ainahin ranar da jirgin saman Najeriya zai fara aiki, minsitan ya ce:

"Kafin karshen gwamnatin nan, kafin ranar 29 ga watan Mayu, za mu tashi sama."

Ya kara da cewar gwamnatin tarayya za ta bar ma'aikatar sufurin jiragen sama fiye da yadda ta same ta kasancewar an cimma fiye da 90% na taswirar hanyoyin sufurin jiragen sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng