A Majami'a Nake Kwana: Miji Ya Roki Kotu Ta Kashe Aurensa Saboda Barazanar Kisa da Matarsa Ke Masa

A Majami'a Nake Kwana: Miji Ya Roki Kotu Ta Kashe Aurensa Saboda Barazanar Kisa da Matarsa Ke Masa

  • Wani mutum mai suna Abiodun Akinyemi ya roki kotu da ta raba aurensa da matarsa saboda cin zarafi
  • Akinyemi ya fada wa kotun yadda ya bar gida na tsawon lokaci yana kwana a majami’a don gudun bala'in matar
  • Ya ce duk da haka bai tsira ba don har wurin aikinsa tana zuwa tare da yi masa barazana ga rayuwarsa

Jihar Osun - Wani mutum mai suna Abiodun Akinyemi ya roki wata kotun al’ada da ta raba aurensa wanda suka shafe shekaru 18 da matarsa saboda barazanar kisa da take masa.

Kotun wadda ke zamanta a Mapo Grade ‘A’ da ke Ibadan babban birnin jihar Osun, ta saurari karar, inda Mista Akinyemi ya ce ya gaji da zama da matar.

Kotun Al'ada a Najeriya
Kotu a Najeriya. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Daily Nigerian ta tattaro yadda Akinyemi wanda ke rayuwa a Olodo ya fada wa kotun cewa:

Kara karanta wannan

Saura Kwana 6: Na Matsu Na Gama Mulkina Saboda Matsin Lamba, Buhari Ya Koka Kan Yawan Tarurruka

“Dole na gudu na koma majami’a saboda ba zan iya jure tsananin cin zarafin da matar ke yi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ya mai shari’a, rayuwa ta min kullin goro tun bayan da na auri Christiana shekaru 18 da suka wuce, har ma wurin aikina take zuwa don ta hargitsa min lissafi da kuma cin zarafi."

Na koma majami'a

Ya kara da cewa:

“Saboda gudun tashin hankali, na gudu na koma majami’a da kwana amma Christiana ba ta bar zuwa har wurin tana cin zarafi na ba.
“Abin takaici, Christiana har barazanar kisa take mini kullum, ni yanzu na gaji ba zan iya ci gaba da zama da ita ba, ba na sha’awar kasancewa da ita.

Mai karar ya roki kotun ta bashi kulawar 'ya'yansu

“Ina rokon kotu da ta mallakar min da kulawar yaranmu a hannuna kuma ta umarceta ta bar mini gida."

Kara karanta wannan

Biyu Babu: Kotu Ta Datse Igiyar Auren Malamin Addini Saboda Yawan Jibgar Matarsa, An Mallaka Wa Matar Dukkan Kadarorinsa

Matar ta maida martani kan tuhumarta da ake

A martaninta, Christiana ta ce mijinta ba mutumin kirki ba ne, ta kara da cewa Faston shi ya fada masa cewa ita ce silar shiga damuwarsa da kuma bala’in da yake fama da su, cewar Daily Post.

Ta kara da cewa kuma ba ya kula da yaransu ko kudin makaranta ba ya iya biya musu, shi yasa ma ta je wurin shi lokacin da ba ta ganshi ba don koka masa cewa yaran suna bukatan wani abu.

Bayan sauraran koke-koken nasu, mai shari’a S.M Akintayo ta shawarci mai karar da wadda ake karar da su rungumi zaman lafiya a tsakaninsu.

Akintayo ta dage sauraran karar har zuwa ranar 3 ga watan Agusta don ci gaba da shari’ar.

Kotu Ta Datse Igiyar Auren Fasto Saboda Jibgar Matarsa, An Mallakar Mata da Dukiyansa

A wani labarin, wata kotu dake zaman ta a jihar Edo ta tsinka igiyar auren Fasto saboda cin zarafi.

Faston mai suna Oni Muyiwa ya kasance yana cin zarafin matar yadda yaga dama har da barazana ga rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel