Jikan Sarkin Kagarko Ya Kubuta Daga Hannun ’Yan Bindiga Bayan Ya Gane Wasu Daga Cikinsu

Jikan Sarkin Kagarko Ya Kubuta Daga Hannun ’Yan Bindiga Bayan Ya Gane Wasu Daga Cikinsu

  • Daya daga cikin iyalan sarkin Kagarko da aka sace kwanakin baya ya tsere daga hannun ‘yan bindiga
  • Yusuf mai shekaru 15 ya tsere ne daga hannun ‘yan bindigan bayan sun tafi dashi don su kashe shi a daji
  • Magatakardan sarkin Kagarko, Yahaya Ibrahim ya tabbatar da faruwar hakan inda ya ce Yusuf yana gida

Jihar Kaduna - Daya daga cikin jikokin Sarkin Kagarko da aka sace a makwanni biyu da suka wuce ya tsere daga hannun ‘yan bindigan bayan shugaban ‘yan ta’addan ya umarci a kashe shi.

Wanda ya tseren Yusuf Sa’ad mai shekaru 15 yana daya daga jikokin Sarkin Kagarko Alhaji Sa’ad Abubakar da aka sace a ranar Lahadi 4 ga watan Mayu, ‘yan bindigan sun sace ‘ya’yan sarkin tare da jikokinsa a harin.

'yan bindiga
Yaro ya Kubuta Daga Hannun ’Yan Bindiga a Kaduna. Hoto: Daily Post
Asali: Twitter

Da yake tabbatar da tserewar yaron, daya daga cikin hadiman sarkin duk da cewa ba a bashi daman yin magana ba ya ce Yusuf ya tsere ne daga hannun ‘yan ta’addan a ranar Juma’a da yamma, cewar jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yadda Muka Rasa ’Yan Uwanmu a Harin ’Yan Bindiga, Mutane Sun Koka a Jihar Plateau

'Yan bindigan sun shiga rudani

Ya kara da cewa, ‘yan bindigan sun gagara samun natsuwa lokacin da suka fahimci Yusuf ya gane wasu daga cikinsu, sai shugabansu ya umarci daya daga cikin ‘yan bindigan ya shiga daji da Yusuf ya kashe shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

“Hankalinsu ya tashi bayan sun fahimci Yusuf ya gane wasu daga cikinsu da kuma shugabansu, sai suka umarci a dauke shi a babur a tafi dashi wuri mai nisa a cikin daji a kashe shi.
“Yusuf ya ce musu yana son yayi fitsari lokacin ‘yan bindigan suna shan taba sai ya tsere.”

'Yan ta'adda na bukatar makudan kudade

Da aka tambaye shi ko sun kira ‘yan ta’addan? Hadimin sarkin ya ce tabbas ‘yan ta’addan sun bukaci makudan kudade a wurinsu.

Ya kara da cewa:

“Tabbas mun yi magana da su kuma sun bukaci makudan kudade, amma tsaro bazan iya fadan yawan kudin ba.”

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dagaci da Wasu Mutane 3 a Jihar Niger

Bayanai daga fadar sarki

Magatakardan sarkin, Yahaya Ibrahim shi ma ya tabbatar da tserewar yaron da kuma kudaden da ‘yan bindigan suka nema.

Magatakardan yace:

“Yusuf ya tsere daga hannunsu kuma yanzu haka yana gida, amma bazan iya fadan yawan kudin da suka nema ba saboda dalilai na tsaro.”

Rundunar 'yan sanda ba ta ce komai ba

Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Muhammad Jalige bai amsa kiran wayan da aka yi masa ba kuma bai maida martani a sakon kar ta kwana da aka tura masa ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoton.

Yan Bindiga Sun Sace 'Ya'ya da Jikokin Sarkin Kagarko a Kaduna

A wani labarin, wasu 'yan bindiga sun kutsa kai cikin fadar sarkin Kagarko tare da sace 'ya'yansa da jikokinsa.

'Yan bindigan sun yi awon gaba da 'ya'ya da jikokin sarkin akalla mutum tara da kuma wasu mutane uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel