Ayarin Motocin Gwamnan Ebonyi Sun Gamu da Hatsari, Mutum Uku Sun Mutu

Ayarin Motocin Gwamnan Ebonyi Sun Gamu da Hatsari, Mutum Uku Sun Mutu

  • Ayarin gwamna David Umahi na jihar Ebonyi da wani Babur mai ɗauke da mutane uku sun yi hatsari
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa mutanen da ke kan Babur ɗin duk sun mutu a hatsarin wanda ya auku a Titin zuwa filin jirgi
  • Mataimakin gwamna da Prince Arthur sun je har gidan waɗanda suka mutu gabanin su wuce zuwa Enugu

Ebonyi - Ayarin gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya kaɗe wani Babur mai ɗauke da mutane uku 'yan asalin ƙaramar hukumar Ezza ta kudu kuma gaba ɗayansu Allah ya musu rasuwa.

Rahoton Punch ya ce ɗaya daga cikin motocin ayarin mai girma gwamna ta kaɗe mahaya Babur ɗin a kan titin zuwa filin jirgin saman Muhammadu Buhari na ƙasa da ƙasa.

Gwamna Umahi.
Ayarin Motocin Gwamnan Ebonyi Sun Gamu da Hatsari, Mutum Uku Sun Mutu Hoto: APC Nigeria
Asali: Twitter

Rahotanni sun nuna cewa ayarin gwamnan, jagoran jam'iyyar APC a Ebonyi, sun kai Umahi filin jirgin da ke Onueke, a hanyarsu ta komawa ne suka gamu da wannan tsautsayin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Rigima Ta Barke Tsakanin Tsagin Jam'iyyar Labour Party a Kotun Zabe

Yaushe hatsarin ya auku?

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa lamarin ya auku ne bayan kaddamar da wata gada, wacce aka raɗa wa suna, "Prince Arthur Eze," a yankin Abaomege, ƙaramar hukumar Onicha.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yarima Arthur Eze da mai girma gwamna Umahi ne suka kaddamar da gadar a jihar wacce ke shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya.

Daga nan kai tsaye gwamna Umahi ya wuce filin jirgin sama, ya bar jihar zuwa birnin tarayya Abuja bayan kammala kaddamar da gadar.

Wane koƙari gwamnati ta yi bayan kaɗe mutanen?

Jaridar Independent ta rahoto cewa daga wurin da haɗarin ya auku, mataimakin gwamna, Eric Kelechi Igwe, da Prince Arthur Eze, suka wuce kai tsaye zuwa gidan iyalan mamatan.

Bayan nan suka umarci a kai gawarwakin mutanen uku ɗakin ajiyar gawa na Asibiti sannan suka wuce zuwa jihar Enugu.

Kara karanta wannan

"Za Mu Sake Dawowa": Gwamna Ganduje Ya Sha Muhimmin Alwashi Ga Kanawa

Motar da haɗarin ya shafa da kuma babur ɗin mutane uku, waɗanda suka rasa rayuwarsu duk sun lalace.

A wani rahoton kun ji cewa Gwamna Zulum Ya Yi Fatali da Shirin Gwamnonin Arewa 5, Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Baya a Majalisa Ta 10.

Farfesa Babagana Zulum ya ce duk da akwia ɗan asalin jihar Borno da ke nemna takara amma ya zaɓi goyon bayan waɗanda jam'iyyar APC ta zaɓa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel