Motar Bas Da Ta Dauko Daliban Najeriya Daga Sudan Ta Kama da Wuta

Motar Bas Da Ta Dauko Daliban Najeriya Daga Sudan Ta Kama da Wuta

  • Motar Bas da ta ɗauko daliban Najeriya daga Sudan zuwa tashar jirgin ruwa ta kama da wuta a kan hanya ranar Litinin
  • Babu wanda ya ji rauni ko da kwarzane kuma tuni suka ci gaba da tafiyar bayan gari ya waye
  • Gwamnatin tarayya ta ci gaba da aikin jigilar yan Najeriya mazauna Sudan a rukuni na biyu

Ɗaya daga cikin Motocin Bas-Bas da ke aikin kwashe daliban Najeriya da suka maƙale a Khartoum, babban birnin ƙasar Sudan ta kama da wuta da safiyar Litinin.

Daily Trust ta tattaro cewa Motocin Bas din na jigilar ɗaliban Najeriya daga Khartoum zuwa tashar jiragen ruwa ta Sudan, inda za'a kwashe su zuwa Saudiyya.

Motar Bas.
Motar Bas Da Ta Dauko Daliban Najeriya Daga Sudan Ta Kama da Wuta Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa Motocin Bas 26 ɗauke da Ɗalibai yan asalin Najeriya da suka maƙale, sun tashi daga Al Razi da misalin karfe 12:00 na tsakar daren yau Litinin zuwa tashar jiragen ruwa.

Kara karanta wannan

Shiri Ya Lalace: Miyagun 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wasu Malaman Addini Cikin Tsakar Dare

"A rukuni na biyu na kwashe yan Najeriya daga Sudan, ɗaya daga cikin motocin Bas, ɗauke da daliban Najeriya 50 daga Sudan mai lambar 'Katsina 1' ta lalace a hanyar zuwa tashar jirgin ruwa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shugaban ƙungiyar dattawan Najeriya mazauna Sudan, Dakta Hashim Idris Na'Allah, na ɗaya daga cikin Fasinjojin motar, wacce ta ɗebo ɗalibai 50 maza 49 da mace ɗaya."
"Lamarin ya faru da karfe 2:30 na daren Litinin agogon Sudan. Direban ya tsaya a kusa da shingen RSF, mintuna kaɗan gabanin tayar Bas ɗin, wacce ta ɗau zafi ta tashe, wuta ta kama."

- Inji Sani Aliyu, wanda ke zaune a Sudan.

Wane ɓarna matsalar ta haifar?

Aliyu ya ƙara da cewa:

"Baki ɗaya mutanen cikin motar sun fita lafiya, ba wanda ya ji ko kwarzane. Daga baya aka raba wa sauran motocin Bas ɗin mutum 40 cikin 50 da Motar ta kwaso, sauran 10 da Direba ana suka kwana a inda lamarin ya faru."

Kara karanta wannan

Rikicin Sudan: An Hana Daruwan Dalibai 'Yan Najeriya Tsallakawa Zuwa Kasar Egypt, Dalilai Sun Bayyana

"Sauran ɗalibai 10 sun ce jami'an RSF sun taimaka musu sosai kuma su suka basu abin kari da safe kafin su bar wurin."

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tuni ɗaliban suka ci gaba tafiya zuwa tashar jirgin ruwa domin komawa gida Najeriya.

Sojoji sun ceto karin dalibar Chibok

A wani labarin kuma Sojoji Sun Ƙara Samun Gagarumar Nasara Bayan Shekaru 9 a Jihar Borno

Sojoji sun samu nasarar ceto ƙarin dalibar Chibok a wani samame da suka kai yankin Lagara a jihar Borno.

Ɗalibar mai suna Hauwa, ta kubuta ɗauke da juna biyu da kuma ɗiyarta mai suna Fatima, wacce ta haifa a hannun 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel