BUA: Jerin Makarantu 22 da Attajirin Kano, Ya Rabawa Tallafin Naira Biliyan 22

BUA: Jerin Makarantu 22 da Attajirin Kano, Ya Rabawa Tallafin Naira Biliyan 22

  • Gidauniyar Abdul Samad Rabiu Africa initiative za ta tallafawa wasu makarantu da Naira biliyan 22
  • Sanarwar ASR Africa ta nuna kowace makarantar za ta amfana da Naira miliyan 250 daga kudin
  • Edidiong Idang ya ce a cikin makarantun da za su ci moriyar kudin akwai jami’o’i da kwalejoji

Abuja - Manyan makarantun gaba da sakandare 22 da ke kasar nan suka amfana da tallafin Abdul Samad Rabiu Africa initiative a shekarar nan.

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa shahararren mai kudin nan, Abdul Samad Rabiu ya rabawa wadannan makarantu tallafin Naira biliyan 22.

Edidiong Idang na ASR Africa ya bada sanarwar cewa kowace makaranta za ta tashi da Naira miliyan 250 a karkashin wannan tsari na ilmi.

Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu ya fito da tsarin ASR Africa domin bada tallafi a bangarorin ilmi, kiwon lafiya da cigaban al’umma.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Bayyana Koma Bayan da Rashin Lafiyar Shugaba Buhari Ta Jawo a Najeriya

Tasirin ASR Africa a Kasashe

Mista Edidiong Idang ya ce za su hada kai da gwamnatoci da kamfanoni masu zaman kansu wajen bunkasa ilmi a Najeriya da kasashen Afrika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto Idang yana mai cewa su na ganin ya zama dole mutanen Afrika su tashi tsaye domin ceton nahiyar daga halin tabarbarewar da ake ciki.

Abdul Samad Rabiu
Alhaji Abdul Samad Rabiu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Baya ga taimako ta fuskar aiki da ASR Africa take badawa, su kan bada gudumuwar kudi.

Manyan jami’o’in tarayya da aka zaba domin su ci moriyar tallafin sun hada da na Jos, Kano, Akwa Ibom, Kogi, Neja, Minna, Owerri da sauransu.

Haka zalika an zabi wasu kwalejojin ilmi da jami’o’in jihohi da kuma makarantar sojoji ta NDA. Sannan akwai wasu jami’o’in ‘yan kasuwa uku.

Jerin makarantun da za su amfana da tallafin sun hada da:

1. University of Uyo

2. University of Jos

Kara karanta wannan

Ana Saura Kwanaki 50 Ya Bar Aso Rock, An Yi Karar Shugaba Buhari da NBC a Kotu

3. Nigerian Law School (Lagos)

4. Federal College of Education Technology, Gusau

5. Federal University Lokoja

6. Federal University of Petroleum Resources, Effurun

7. Nasarawa State University

8. University of Lagos

9. University of Port Harcourt

10. Federal University of Technology Minna

11. Uthman Dan Fodio University

12. Bayero University Kano

13. Adamawa State University

14. Babcock University

15. Federal University, Gashua

16. Federal University of Technology Owerri

17. Al-Qalam University

18. National Institute for Policy and Strategic Studies, Kuru

19. Baze University

20. Nigerian Defence Academy

21. Crescent University

22. Michael Okpara University of Agriculture, Umudike

Wasikar Chimamanda Adichie

Rahoto ya zo cewa Chimamanda Adichie ta fito ta rubuta budaddiyar wasika ga Shugaba Joe Biden na kasar Amurka a game da zaben Najeriya.

A wasikar da ta zagaya Duniya, marubuciyar ta zargi INEC da magudi a zaben da APC ta ci. Adichie ta koka a kan yadda aka hana Peter Obi kai labari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng