Buhari Zai Kai Ziyarar Kwana 8 A Kasar Saudiyya, Zai Yi Umrah

Buhari Zai Kai Ziyarar Kwana 8 A Kasar Saudiyya, Zai Yi Umrah

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi balaguro zuwa kasar Saudiyya inda zai shafe kwana takwas
  • Buhari, wanda wasu cikin hadiminsa za su yi masa rakiya zai kai ziyarar aiki ne tare da yin Umrah
  • Wannan ce za ta kasance ziyara ta karshe da Buhari zai kai Saudiyya a matsayinsa na shugaban kasa

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata da safe, zai kama hanya zuwa kasar Saudiyya inda ake sa ran zai yi kwana takwas ya kuma yi Umrah, The Punch ta rahoto.

Garba Shehu, babban hadimin shugaban kasa na musamman kan watsa labarai, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Buhari
Buhari Zai Kai Ziyarar Kwana 8 A Kasar Saudiyya, Zai Yi Umrah. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Wani sashi na sanarwar ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Takarar Majalisa ta Dauki Zafi, Ana Sauraron Dawowar Tinubu Bayan Kwana 18 a Kasar Waje

"Buhari zai tafi Saudiyya a wata ziyarar aiki daga ranar Talata 11 zuwa 19 ga watan Afrilu a ziyarsa ta karshe a matsayin shugaban kasa, inda zai gudanar da aikin Umrah."

A sanarwar da ya fitar a yammacin ranar Litinin mai taken 'Buhari zai tafi Saudiyya don ziyarar aiki,' Shehu ya ce wasu cikin hadiman shugaban kasar za su yi masa rakiya.

Wannan shine ziyarsa ta shida kuma ta karshe zuwa kasar ta Saudiyya tun bayan zamansa shugaban kasa a 2015.

Wasu cikin kasashen da Buhari ya ziyarta a bayan zama shugaban kasa

Daga cikin fiye da kasashe 40 da Buhari ya ziyarta a matsayin shugaban kasa, wadanda ya fi zuwa suna Amurka, Birtaniya, Saudiyya, Afirka ta Kudu da Faransa.

Ya kuma ziyarci Habasha sau biyar ya ziyar Hadadiyar Daular Larabawa, UAE, Ghana, Nijar da Senegal sau uku kowannesu.

Kasashen da ya ziyarta a kalla sau biyu sun hada da China, Jamus, Jamhuriyar Benin, Gambiya. Kenya, Equatorial Guinea, Misra, Mali, Chadi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: APC Ta Kori Sanata Da Aka Zaba A Karon Farko, Ta Bada Kwararan Dalilai

Shugaban kasar ya kuma ziyarci kasashen Kamaru, Côte d’Ivoire, India, Sudan, Spain, Iran, Malta, Rwanda, Qatar, Turkey, Scotland, Morocco, Poland, Portugal, Russia, Jordan, Burkina Faso, Belgium, Liberia da Japan; jimillar fiye da kasashe 40 da kimanin tafiye-tafiye 90 zuwa kasashen waje.

Na Kosa In Sauka Daga Mulki, Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce sake jadada niyarsa na barin gadon mulki da zarar wa'adinsa ta cika.

Shugaban kasar a baya ya sha nanata cewa ya kosa ranar 29 ga watan Mayu ta yi ya tattara kayansa ya koma gona da dabobinsa.

Buhari ya yi wannan furucin ne lokacin da ya ke bankwana da jakadiyar Amurka mai barin gado, Mary Beth Leonard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel