Gwamnatin Kaduna Ta Dawo Da Malaman Firamare 1,288 Da Aka Kora Wata 10 Kan Faduwa Jarrabawar Gwajin Cancanta
- Gwamnatin Jihar Kaduna ta maido wa malamai firamare 1,288 aikinsu bayan korarsu daga aiki watanni 10 da suka gabata
- An sallami malaman ne kan dalilin faduwa jarrabawar gwajin cancantar aiki da gwamnatin ta gudanar a don yin waje da malamai da ba su san makamashin aiki ba
- Amma daga bisani, wasu cikin wadanda aka kora din sun yi korafi cewa sun ci jarrabawar amma duk da haka aka kore su, hakan yasa aka yi bincike kuma daga baya aka dawo musu da aikinsu
Jihar Kaduna - Gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da dawo da malaman firamare 1,288 da aka kora daga aiki kimanin watanni 10 da suka shude, The Cable ta rahoto.
A watan Yunin 2022, Gwamnatin Jihar Kaduna ta sallami fiye da malamai 2000 a jihar saboda faduwa jarrabawar gwajin cancantar koyarwa.
Kamfanin dillancin labarai NAN ta rahoto cewa Hauwa Mohammed, mai magana da yawun Hukumar Ilimin Firamare na Kaduna, KADSUBEB, ta sanar da cigaban a ranar Laraba.
Hauwa ta ce 1,266 ne jarabawa ta shafa, yayin da 22 aka cire su daga tsarin biyan albashi na jihar saboda wasu zarge zarge.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Idan za a iya tunawa hukumar a watan Yuni 2022 ta kori malaman makarantar firamare 2,357 saboda faduwa jarabawa.
Hukumar ta ce daga cikin adadin, 2,192 aka kora saboda ba su zana jarabawar ba, yayin da 165 aka kore su saboda rashin kwazo.
Dalilan da wasu malaman da aka kora suka bada
Wasu daga cikin malaman da abin ya shafa, sun ce duk da sun ci jarabawar amma an kore su, wasu kuma sun ce ba su da lafiya a lokacin jarabawar tare da gabatar da shaida.
Wasu sun yi korafin cewa suna hannun masu garkuwa lokacin jarabawar; wasu kuma sunce an dakatar da su, wasu kuma sun ce ba sa shiga aji kuma an tsame su daga gudanar da jarabawar.
Ta ce:
"Bayan dubawa tare da tabbatar da korafinsu, gwamnatin jihar ta amince da dawo da malamai 392,wanda su ka lashe jarabawar, da malamai 515 da ba sa shiga aji da aka tsame daga jarabawar.
"Sauran sune: 298 da aka tabbatar ba su da lafiya lokacin jarabawar, da kuma 61 da aka yi garkuwa da su ko su ka gamu da wani hadari wanda sakatarorin ilimin su su ka tabbatar.
"Su ma, malamai 22, da aka cire daga tsarin biyan albashi saboda wasu dalilai su ma an mayar da su aikin, wanda ya zama jimillar 1,288 da aka sake dawo da su."
Jami'ar huldar ta ce ana shawartar duk wanda abin ya shafa su karbi takardar mayar dasu aikin a hannun sakatarorin iliminsu ba tare da bata lokaci ba.
Sallamar Malaman Makaranta Da El-Rufai Ya Yi Ya Saba Wa Doka - NUT
A baya, Ibrahim Dalhatu, kungiyar malaman makaranta, NUT, ta jihar Kaduna ya yi tir da korar malaman makaranta 2,357 a jihar da gwamnati ta yi kan fadi jarrabawar cancanta.
Dalhatu ya ayyana cewa abin da gwamnatin ta yi ya saba wa doka, Vanguard ta rahoto.
Asali: Legit.ng