Akwai Yiwuwar Sanusi II Ya Dawo Bankin CBN a Matsayin Gwamna a Mulkin Tinubu

Akwai Yiwuwar Sanusi II Ya Dawo Bankin CBN a Matsayin Gwamna a Mulkin Tinubu

Ana yada labari cewa wasu sun fara bada shawara gwamnati mai-ci ta dawo da Sanusi Lamido Sanusi

Idan aka yi nasara, Sanusi Lamido Sanusi watau Muhammadu Sanusi zai koma kujerar Gwamnan CBN

A 2014 Goodluck Jonathan ya dakatar da Basaraken daga aiki, sai ya maye gurbinsa da Godwin Emefiele

Abuja - Akwai kutun-kutun na gaske da ake yi da nufin ganin Sanusi Lamido Sanusi watau Muhammadu Sanusi II ya koma babban bankin kasa na CBN.

Wani rahoto da mu ka samu a Vanguard a daren Laraba, ya tabbatar da akwai wasu manya da suke so a tafi da Muhammadu Sanusi II a gwamnati mai zuwa.

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023 ne Asiwaju Bola Tinubu zai dare kan mulki a matsayin zababben shugaban Najeriya, zai gaji Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Ya Fadi Munanan Barazanar da Ake Fuskanta a Yau a Najeriya

Ana tunanin mutane irinsu Mai girma Nasir El-Rufai su na goyon bayan Sanusi II, shugaban kasa mai jiran gado yana sauraron maganar Gwamnan Kaduna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An yi rashin Sanusi a CBN?

Sanusi Lamido Sanusi wanda masanin tattalin arziki ne ya jagoranci babban bankin tsakanin 2009 da 2014 a lokacin da Goodluck Jonathan ya dakatar da shi.

A lokacin da yake Gwamnan babban banki, Najeriya ta shawo kan matsalar tattalin arzikin da Duniya ta fada 2008/2009, darajar Naira ba ta sukurkuce ba.

Sanusi II
Sanusi Lamido Sanusi da Sarkin Birtaniya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A tsawon shekarun da ya yi a ofis, Sanusi II ya yi kokarin tsaida farashin Dalar Amurka, abin da ya gagari kasar a karkashin jagorancin Godwin Emefiele.

Wata majiya ta ce daga Junairu zuwa Maris, tattalin arzikin Najeriya ya rasa Naira tiriliyan 20, hakan ya jawo abubuwa sun tabarbare musamman a kauyuka.

Rahoton ya ce Tinubu wanda kwararren Akanta ne, zai maida hankali wajen shawo kan matsalar kudi, ya nemi ya bunkasa tattalin arziki da zarar ya shiga ofis.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 3 da Suka Auka Matsalar Zabe Bayan Yin Fito Na Fito da Buhari a Kan Canjin Kudi

Ya za ayi da Godwin Emefiele?

Akwai masu ganin idan Mai martaban ne yake rike da bankin CBN, abubuwa za su gyaru. Inda za a samu cikas, sai a shekarar 2024 wa'adin Emefiele zai kare.

Idan aka yi nasarar dawo da Basaraken, zai bi sahun Godwin Emefiele wanda ya yi wa’adi biyu. Zuwa yanzu ba a ji tsohon Sarkin ya ce komai a kan batun ba.

Leadership ta tabbatar da cewa ana farautar masanin tattalin arzikin, amma 'dan sa ya yi magana a shafin Twitter, ya ce Sanusi II bai da niyyar komawa CBN.

Ashraf Sanusi ya ce Khalifa ya shaidawa zababben shugaban kasar cewa a shirye yake ya shi shawara a kan harkar tattalin arziki, amma bai sha'awar mukamin.

Heritage Times ta karrama GEJ

A karshen makon jiya Heritage Times ta shirya wani biki, kamar yadda rahoto ya zo mana, an ba wasu shugabannin Afrika lambar yabo da kyauta na girma.

Kara karanta wannan

Mazan jiya: Hotunan gidan Tafawa Balewa sun jawo martani mai daukar hankali a intanet

Goodluck Jonathan ya samu kyautan zama Gwarzon Damukaradiyya da Jakadan zaman lafiya. HT ta karrama Marigayi John Magufuli na kasar Tanzaniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng