Yadda Karancin Naira Ya Kashe Kasuwancin Miliyoyin Mutane a ‘Yan Watanni – ASBON

Yadda Karancin Naira Ya Kashe Kasuwancin Miliyoyin Mutane a ‘Yan Watanni – ASBON

  • A dalilin canjin Naira da CBN ya yi a shekarar nan, kusan kamfanoni miliyan 25 su ka mutu a Najeriya
  • ASBON ta ce Gwamnatin tarayya ta jawo kamfanonin MSME miliyan 25 sun shiga wani hali na ha’ula’i
  • Bayan tsawon makonni ba a san inda aka dosa ba, an soke tsarin canjin kudi da aka nemi ayi a kasar

Abuja - Dadewa da aka yi ana fana da karancin Naira ya tilastawa kamfanonin MSME da-dama sun mutu ko kuwa ayyukansu ya yi kasa a Najeriya.

Leadrership ta rahoto kungiyar ASBON ta ‘yan kasuwan Najeriya ta ce kamfanonin kanana da matsakaicin kasuwanci har miliyan 25 tsarin ya shafa.

Gwamnatin taraya ta amince babban bankin CBN ya canza takardun N200, N500 da N1000, a karshe dai kotun koli ta tilasta aka dawo da tsofaffin kudi.

Kara karanta wannan

Ahaf: 'Yan Najeriya sun daina ajiya a banki, bankuna sun koka kan halin da ake ciki

Shugaban ASBON a Najeriya, Dr. Femi Egbesola ya yi magana game da lamarin, ya ce tsarin da aka nemi a kawo ya kara yawan masu zaman banza a kasa.

Kasuwanci miliyoyi ya karye

An rahoto Femi Egbesola yana cewa kusan 60% na kamfanonin kananan kasuwanci da ake da su a Najeriya, sun shiga sahun wadanda suka karairaye.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

ASBON ta ce akwai kamfanonin MSME miliyan 40 da aka yi wa rajista, adadin wadanda tsarin canjin kudi ya yi wa mugun tasiri sun kai miliyan 25.

Bankin CBN
Taron shugabannin bankin CBN Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Egbesola yake cewa ba komai ya jawo miliyoyin mutane suka rasa hanyar neman abincinsu ba illa rashin kwarewa a wajen amfani da kafafe na zamani.

Shugaban na ASBON ya ce kamfanonin da canjin ya shafa ba su da kwarewa wajen sanin kan kudi.

A dalilin wannan tsari na gwamnati da ya birkita kasuwanci, kungiyar ta ASBON ta ce saukin kasuwanci da ake takama da shi a Najeriya ya yi kasa.

Kara karanta wannan

IPAC Ta Yi Martani Yayin da DSS Ta Gano Masu Yunkurin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi

Ya za a gyara matsalar?

Duk da matsalolin da aka samu a bana, ‘yan kasuwan sun yi kira ga gwamnati ta nada wadanda suka san kan harkar neman kudi wajen jagorantar SME.

Idan ana so a magance matsalar da aka shiga, Dr. Egbesola ya ce wajibi ne hukuma ta zauna da masu ruwa da tsaki wajen kawo tsare-tsaren da za su agaza.

Zaben Gwamnonin bana

A bangaren siyasa, mun kawo rahoto cewa za a iya cewa Mohammed Bago, Umar Namadi, Dikko Radda, da Hyacinth Alia sun ci zabe cikin sauki a takarar 2023.

Amma a Zamfara, Kano da Bauchi, Jam’iyyun adawa sai da suka yi da gaske kafin su iya doke APC. NNPP ta fizge mulkin Kano a hannun APC bayan shekaru takwas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng