Buhari, Osinbajo, Tinubu, Shettima da Sauran Jami’an Gwamnati Za Su Bayyana Kadarorinsu

Buhari, Osinbajo, Tinubu, Shettima da Sauran Jami’an Gwamnati Za Su Bayyana Kadarorinsu

  • Hukumar kula da da’ar ma’aikata (CCB) ta bukaci shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo da su bayyana yawan kadarorinsu yayin da suke shirin barin ofis
  • Hakazalika, hukumar ta bukaci dukkan gwamnoni masu barin gado, hadiman shugaban kasa, ministoci ‘yan majalisu da shugabannin kananan hukumomi duk su yi hakan
  • Hukumar ta CCB ta kuma bayyana cewa, wannan umarni ya shafi shugaban kasa mai jiran gado Bola Tinubu da mataimakinsa da sauran wadanda za su fara aiki ga jama’a

FCT, Abuja Yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kokarin barin ofis da shi da mataimakinsa Osinbajo, dole za su bayyana adadin kadarorinsu nan da 29 ga watan Mayu.

Wannan ya shafi dukkan ministoci 44 da gwamanoni masu barin gado a shirin kasar na karbar sabbin masu tafiyar da lamuran al’umma.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnoni 36 Za Su Gana Da EFCC, CBN Don Yanke Shawara Kan Kudin Tsaro

Wannan batu na fitowa ne daga bakin Mustapha Musa, mai ba shugaban hukumar kula da da’ar ma’aikata ta CCB shawari kan ayyuka gama-gari.

Su Buhari za su bayyana adadin kadarorin da suka tara
Shugaban kasa Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Rahoton jaridar Punch ya ce, Musa ya tabbatar da cewa, an kammala shirin ba da fom na bayyana kadarorin ga dukkan manyan jami’an gwamnati da ke shirin tafiya da masu shigowa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kuma tattaro cewa, cike wannan fom na kadarori bai tsaya kan su Buhari ba, ya shafi hadimansa, ‘yan majalisun jiha da na tarayya da ma sanatoci har kan shugabannin kananan hukumomi.

Tinubu da Shettima na da kwanaki 90 na bayyana adadin kadarorinsu

A bangare guda, zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da gwamnoni 28 masu shigowa su ma za su cike wannan fom din.

Kamar yadda Legit.ng ta tattaro, CCB za ta ba su Tinubu wa’adin watanni uku na cike wannan fom na bayyana adadin kadarori.

Kara karanta wannan

IPAC Ta Yi Martani Yayin da DSS Ta Gano Masu Yunkurin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi

A cewar Musa:

“Ana tsammaninsu (jami’ai) da su bayyana dukkan kadarorinsu a lokacin da za su shiga da kuma lokacin da za su bar ofis. Abin da doka ta tanada kenan.
"Za su dawo da fom din da suka cike a lokacin da za su bar ofis, ba za ka cika fom din bayyana kadarori ba alokacin da kake ofis.
“Haka yake, a lokacin shiga da kuma fita. Haka kundin tsarin mulkin kasa yace, haka kuma kundin dokar da’ar ma’aikata ya fadi a sashe na 15. Wannan kuma ya shafi wadanda ke zuwa cikin gwamnati amma su suna da watanni uku na bayyana kadarorinsu.”

A bangare guda, jama'a sun shiga mamaki bayan ganin irin gidan da tsohon firayinministan Najeriya, Tafawa Balewa ya rasu ya bari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.