Gwamnati ta Saki Sabon Bayani Akan Farashin Motocin Belgium a Najeriya

Gwamnati ta Saki Sabon Bayani Akan Farashin Motocin Belgium a Najeriya

  • Sabon Rahoton yace darajar motocin takumbo a Najeriya yayi kasa da kaso 50 cikin dari
  • Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ce ta sanar da wannan yanayin na saukar farashin motocin Tokumbo
  • Dilolin mota daga kasashen waje sun sanar da cewa, kamfanonin jigilar motoci sun rage shigo musu da motoci zuwa Najeriya

Abuja - A wani sabon rahoton hukumar samar da kidigdiga ta kasa (NBS) ta fitar, tace darajar motocin da akai amfani dasu da ake kira “motocin tokumbo” sun yi matukar sauka daga kaso 47 a cikin dari a 2022.

Kamar yadda hukumar ta bayyana, darajar saukar na tokumbo na nufin duk kudaden da ake siyan tokunbo gabaki daya a Najeriya ya sauko daga Biliyan N617.48 a shekarar 2021 zuwa Biliyan N335.05 a shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Cafke Wani Ɓarawo Da Aka Daɗe Ana Nema A Jihar Arewa, An Ƙwato Motocci Daga Hannunsa

Alkaluman na NBS sun kara da fadin cewar, motocin tokumbo an sake kashe wajen biliyan N72.32 wajen shigo dasu a watanni tsakanin janairu zuwa Maris na shekarar 2022.

Motocin tokunbo
Gwamnati ta Saki Sabon Bayani Akan Motocin Tokunbo a Najeriya, Farashin Su Ya Sakko da Kaso 47 Cikin Dari
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkaluman sun kara nuna cewar a watanni Aprilu zuwa Yuni an siyo motocin tokunbo na Biliyan N96.76, wanda a watannin Yuli zuwa Satumba aka sake kasha biliyan N90.77.

An kuma kashe biliyan N65.19 a tsakanin Satumba zuwa Disemba wajen sayo motocin tokunbo wanda hakan ke nufin an kashe adadin biliyan N325.05 wajen shigowa da motocin na tokunbo.

Idan aka hada da shekarar 2021, an samu an shigo da motocin tokumbo na biliyan N174.22 a Janairu-Maris, sai aka kara shigo da motoci na biliyan N172.07 billion a Afrilu zuwa Yuni.

An sake shigo da motoci na biliyan N185.41 a Yuli-Satumba, sai kuma akashigo da motoci na na tokumbo na adadin biliyan N85.77 a Satumba zuwa Disemba a 2021 wanda jumulla yayi daidai da adadin biliyan N617.84.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Amurka ta Karbe Naira Biliyan 25 Daga Hannun Tsohuwar Ministar Najeriya

A takaice dai:

2021 (Adadin biliyan N617.84) 2022 (Adadin biliyan N325.05)

1. Janairu Zuwa Maris N174.22 1. Janairu Zuwa Maris N72.32

2. Afriku Zuwa Yuni N172.07 2. Afriku Zuwa Yuni N96.76

3. Yuli Zuwa Satumba N185.41 3. Yuli Zuwa Satumba N90.77

4. Satumba Zuwa Disemba N85.77 4. Satumba Zuwa Disemba N65.19

Business Reports ta ruwaito cewar, masu saro motocin sun yi korafi akan saukar sayen motocin.

Inda suka ce, hakan ya samo asali ne abisa yadda ake cajin su da kwastam suke na kudin shigo da kaya mai yawan gaske.

Sun kuma alakanta saukar sayan motocin tokumbo akan rashin tsayawar dala waje daya da kuma faduwar darajar naira.

Masu saida motoci sun ce, tunda hukmar kwastam ta zabga kudin shigo da kaya, aka samu saukar adadin motocin tokumbo da ake shigowa dasu Najeriya kamar yadda Nairametrics suka ruwaito.

Kara karanta wannan

Bankuna Zasu Kara Adadin Yawan Kudin da Mutane Zasu Iya Cira Daga ATM da Cikin Banki

Idan za’a iya tunawa a watan Afrilu na 2022, hukumar kwastam ta Najeriya ta sanar da Karin kudin da take cajar masu shigo da motoci Najeriya da kaso 20% cikin dari wanda yazo daidai da Muradin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma.

Motocin Tokunbo Zasu Kara Farashi Abisa Sabon Cajin Hukumar Kwastam

A wani rahoto mai kama da wannan, tuni jaridar Legit.ng ta ruwaito cewar, motocin da akayi amfani da su farashin sun a shirin yin tashin gwauron zabi abisa wani sabon tsarin haraji da hukumar kwastam take shirin kaddamar wa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel