Anyi Babban Rashi: Tsohon Alkalin Alkalan Musulunci a Jihar Kwara Ya Rasu

Anyi Babban Rashi: Tsohon Alkalin Alkalan Musulunci a Jihar Kwara Ya Rasu

  • Allah ya yiwa tsohon alƙalin alƙalan musulunci na jihar Kwara, mai shari'a Abdulmutallib Ahmad Ambali rasuwa
  • Marigayi mai shari'a Abdulmutallib Ahmad Ambali ya rigamu gidan gaskiya ne bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya
  • An bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki mai riƙo da koyarwar addinin musulunci a lokacin rayuwar sa

Jihar Kwara- Tsohon alƙalin alƙalan kotun ɗaukaka ƙara ta shari'ar musulunci a jihar Kwara, mai shari'a Abdulmutallib Ahmad Ambali, ya rasu.

Marigayin ya rasu ne a safiyar ranar Alhamis a asibitin koyarwa na jami'ar Ilorin (UITH), Oke-Oyi, bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekara 83 a duniya. Rahoton Daily Trust.

Kwara
Anyi Babban Rashi: Tsohon Alkalin Alkalan Musulunci a Jihar Kwara Ya Rasu Hoto: Naija News
Asali: UGC

Marigayin shine alƙalin alƙalai na biyu bayan mai shari'a Abdulkadir Orire, kuma rajistara na farko a kotun ɗaukaka ƙara ta shari'ar musulunci a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan 2023: Taya Murnar Nasir Yusuf Gawuna Ga Abba Kabir Yusuf Gida-Gida

Marigayi Abdulmutallib Ahmad Ambali ya kwashe shekara 8 a kujerar alƙalin alƙalan daga shekarar 2001 zuwa 2008.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wata tattauna ta wayar tarho da Daily Trust, alƙalin alƙalan musulunci na jihar Kwara, mai shari'a Abdullateef Kamaldeen wanda ya tabbatar da rasuwar, ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai tsoron Allah, haziƙin alƙali wanda yayi riƙo da koyarwar addinin musulunci.

Mai shari'a Kamaldeen yace:

“Duba da ya rasu a cikin watan Ramadana muna masa kyakkyawan fatan samun rahama, muna addu'ar Allah ya jiƙansa da rahama ya sanya aljannah ta zama makoma a gare sa."

Ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirkiri, mai riƙo da addini, mai kyawawan halaye wanda baya raina kowa. Rahoton Naija News

Mutum ne mai mayar da hankali a kowane lokaci. Tabbas jihar Kwara tayi asarar babban alƙali kuma malami. Shi komai ne a waje na, malami na ne wanda nake koyi da shi." Inji shi

Kara karanta wannan

Malamin Addinin Musulunci Ya Dau Zafi Ya Bayyana Illar Makarkashiyar Hana Rantsar Da Tinubu

Mai shari'a Kamaldeen ya bayyana cewa marigayin ya fara rashin lafiya ne a ranar Lahadi da ta gabata, inda aka kai shi asibitin Olalomi daga nan aka tafi da shi asibitin koyarwa na jami'ar Ilorin (UITH), inda a nan Allah ya karɓi rayuwar sa.

Na'ibin Limamin Masallacin Sultan Bello Ya Rasu

A wani rahoton da muka kawo muku a baya, kun ji cewa Allah ya yiwa mataimakin limamin masallacin Sultan Bello dake Kaduna rasuwa.

Marigayin Mallam Ibrahim Isa ya rasu ne a wani asibiti a cikin birnin Kaduna bayan ƴar gajeruwar jinyar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel