Hadimin Gwamna da Aka Yi Garkuwa da Shi a Ramadan Ya Biya Kudi, Ya Fanshi ‘Yanci

Hadimin Gwamna da Aka Yi Garkuwa da Shi a Ramadan Ya Biya Kudi, Ya Fanshi ‘Yanci

  • Kwanaki aka dauke wani Mai ba Gwamnan Zamfara shawara na musamman a kan siyasa
  • Yanzu maganar da ake yi, Ibrahim Ma’aji ya kubuta daga hannun ‘yan bindiga bayan an kai kudi
  • ‘Yanuwan wannan Bawan Allah sun tabbatar da cewa sai da aka biya kudi sannan aka fito da shi

Zamfara - Ibrahim Ma’aji wanda yana cikin masu ba Gwamna Muhammad Bello Mattawalle shawara na musamman, ya dandana iskar ‘yanci.

A makon da ya gabata ne wasu miyagun ‘yan bindiga su ka dauke Ibrahim Ma’aji da nufin samun kudin fansa, Punch ta ce a halin yanzu ya kubuta.

Alhaji Ma’aji wanda aka dauke kwanakin baya yana shirin komawa gaban iyalinsa bayan ya yi kwanaki kusan uku ‘yan bindiga su na tsare da shi.

Rahoton ya ce yanzu haka Hadimin Gwamnan na jihar Zamfara yana babban asibitin tarayya da ke garin Gusau domin a tabbatar da lafiyar jikinsa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun harbe jami'an gwamnati na NSCDC 3, a wata jiha

S.A yana kwance a FMC Gusau

Kamar yadda aka saba, idan mutum ya tsira daga hannun ‘yan bindiga, a kan kai shi asibiti domin likitoci su duba lafiyarsa har ya fara murmurewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma’aji wanda ya yi rashin sa’a, ya fada hannun masu garkuwa da mutane, shi ne mai rike da ofishin mai ba Gwamna shawara kan harkokin siyasa.

Sojoji
Sojojin Najeriya a jeji Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A ranar Asabar ne ‘yan bindiga suka shiga har gidan wannan Bawan Allah a unguwar Mareri da ke birnin Gusau, jaridar ta ce Talata ya fito.

Sai da aka biya kudi tukuna

Mohammed Ahmed wanda ‘danuwan Hadimin Gwamnan na Zamfara ne, ya ce ‘yan bindigan sun karbi makudan kudi kafin su yarda su sake shi.

Amma Mohammed Ahmed bai fadawa ‘yan jarida hakikanin abin da aka biya a matsayin fansa ba, an iya gano cewa ba kubutar da shi aka yi ba.

Kara karanta wannan

Kasar Ingila ta Kakaba Takunkumi a kan ‘Yan Siyasa 10 a Najeriya Saboda Kalamansu

“An ba su wasu kudi bayan an yi ta kai ruwa rana ana tattaunawa, a karshe sai suka fito da shi.”

- Mohammed Ahmed

Da aka tuntubi Mai magana da yawun bakin ‘yan sanda na reshen jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu domin jin ta bakinsu, ba a same shi a waya ba.

Zaben Zamfara a 2023

Bello Matawalle ya ce motocin sojoji 300 aka shiga da su Zamfara lokacin zabe, an ji labari Gwamnan ya ce da karfi da yaji aka doke shi a takarar 2023.

Mai girma Gwamnan Zamfara ya ce ta kai za a samu Sojoji akalla 50 a duk wata rumfar zabe, yana mai kokawa a kan abin da ya faru a zaben bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng