Matashiya: Yadda Jami'ar Chicago ta Tabbatar da Cewa Makarantar Tinubu Ya Halarta

Matashiya: Yadda Jami'ar Chicago ta Tabbatar da Cewa Makarantar Tinubu Ya Halarta

  • Jami'ar Jihar Chicago ta Amurka ta tabbatar da dalibtar Bola Tinubu, zababben
  • Makarantar ta tabbatar da lamarin ne, bayan kafafen yaɗa labarai a Najeriya sun nemi buƙatar hakan
  • Masu ɓukatar labarai a Najeriya sun buƙaci sanin gaskiyar lamari ne bayan zargi yayi yawa akan sahihancin jami'ar Tinubu

A kwanakin baya yan Najeriya suka shiga yunkurin sanin hakikanin ikirarin da zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayi na halartar Jami'ar jihar Chicago.

Yan Jarida sun bazama wajen kawo wa yan Najeriya sahihin bayani akan batun daya tada jijiyar wuya, ya janyo kace nace a fagen siyasar kasa mafi yawa a nahiyar Afirka.

Saboda wannan kokarin ne, jami'ar jihar Chicago dake Amurka, ta tabbatar da batun da ake ta yamaɗiɗi akai kan zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Malamin Addinin Musulunci Ya Dau Zafi Ya Bayyana Illar Makarkashiyar Hana Rantsar Da Tinubu

Certificate Tinubu
Matashiya: Yadda Jami'ar Chicago ta Tabbatar da Cewa Makarantar Tinubu Ya Halarta Hoto: Legit.ng
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'ar ta tabbatar da cewa, tabbas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya halarci makarantar mai daɗaɗɗen tarihi.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewar, Beverly Poindexter ne ya tabbatar da hakan ta wani saƙo da aka aika masa ga imel.

Ita dai Beverly Poindexter shine mai bada sakamakon jarabawar ɗalibai na makarantar, kuma shine mai tantance sahihancin takardun jami'ar.

Ya maida martanin tun talata, 25 ga watan Janairu. Rahoton Legit.ng

Ga abinda Poindexter ya rubuta :

“Tabbas, Mr Tinubu ya halarci makarantar mu, kuma idan ana buƙatar ƙarin bayani a shiga studentclearinghouse.org domin tura buƙatar bayanin a hukumance."

An tabbatar da Tinubu yayi Ɗalibta a Jami'ar Chicago

A wani labari mai kama da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito cewar, tuni jami'ar da Tinubu ya halarta ta tabbatar da cewar, ya halarci makarantar ne daga 1977 zuwa 1979.

Legit.ng ta gano a wata wasiƙa mai kwanan wata Agusta 20, 1999, wacce magatakardan jami'ar ya sanyawa batu hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel