Yan Sandan Katsina Sunyi Musayar Wuta Da Yan Ta'adda, An Sheke Daya, An Kwato AK-47

Yan Sandan Katsina Sunyi Musayar Wuta Da Yan Ta'adda, An Sheke Daya, An Kwato AK-47

  • A wani musayar wuta tsakanin yan sanda da yan bindiga a Jihar Katsina, yan sanda sun yi nasarar halaka daya tare da kwato bindiga
  • Rundunar yan sandan jihar ce ta sanar da haka ta bakin mai magana da yawunta SP Gambo Isah
  • Rundunar ta ce ta yaba da kokarin jami'an, yadda su ka kakkabe yan ta'adda cikin kwarewa da kwazo

Jihar Katsina - Jami'an yan sandan Jihar Katsina sun yi musayar wuta da yan bindiga ranar Litinin a titin Danmusa/Yantumaki a da ke karamar hukumar Danmusa har sun kashe dan ta'adda daya.

Yan sandan sun ce sun kwato bindiga kirar AK-47 lokacin bata kashin, rahoton jaridar The Punch.

Taswirar Katsina
Yan Sandan Katsina Sunyi Musayar Wuta Da Yan Ta'adda, An Sheke Daya, An Kwato AK-47. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Ceto Mutum 13 Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Wata Jihar Arewa

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ranar Talata, ya ce yan bindigar sun tare titin a daidai kauyen Kesassa.

Isah ya ce:

''Ranar 27 ga watan Maris, 2023, da misalin 2:30 na rana, mun samu kiran gaggawa cewa gungun yan ta'adda, su na harbi kan mai uwa da wabi da bindigun AK-47, sun tare titin Danmusa-Yantumaki, da ke karamar hukumar Danmusa a Jihar Katsina.
''Nan take, shugaban ofishin yan sanda na Danmusa, ya jagoranci tawagar yan sanda zuwa yankin, su ka datsi yan ta'addar tare yin nasarar kawar da su.
''A binciken da aka gudanar a wajen, an tsinci gawar dan bindiga daya da aka harbe. Sannan, an samu bindiga kirar AK-47 da jakar harsashi dauke da harsashi 22 ma su rai a wajen.''

Isah ya ce su na hasashen an kashe yan ta'adda da yawa ko kuma sun gudu da munanan raunin bindiga.

''Ana ci gaba da bincike a dajika mafi kusa da nufin kama su a raye ko a mace,'' in ji shi

Kara karanta wannan

Yadda Aka Min Tayin N100m Don In Janye Takara, Dan Shekaru 33 Da Ya Kayar Da Kakakin Majalisar Yobe

Isah ya kuma roki mutanen yankin, da su sanar da yan sanda idan sun hangi wani da irin raunin da su ke zargi.

Ya kara da cewa:

''Rundunar yan sanda ta yaba da kokarin da yan sandan su ka nuna, na kakkabe yan ta'adda cikin salo da kwarewa.''

An Cafke Yan Kungiyar Ta'addanci Da Ke Addabar Nasarawa Da Abuja

A wani rahoton kun ji cewa yan sandan Abuja sun yi nasarar kama mambobin wata mugunyar kungiya da ake zarginsu da adabar mutanen jihar Nasarawa da Abuja.

Sadiq Abubakar, kwamishinan yan sandan Abuja ya ce an cafke wadanda ake zargin ne a wani otel da ke unguwar Masaka a jihar Nasarawa da ke kusa da Abuja, rahoton The Cable.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel