'Yan Sanda Sun Damke Kungiyar 'Yan Ta'adda Dake Addabar Abuja da Nasarawa

'Yan Sanda Sun Damke Kungiyar 'Yan Ta'adda Dake Addabar Abuja da Nasarawa

  • Jami'an rundunar 'yan sandan Babban Birnin Tarayya sun yi nasarar cafke wasu da ake zarginsu da ta'addanci gami da fashi da makami da babban birnin tarayya da jihar Nasarawa
  • Kwamishinan 'yan sandan FCT, Sadiq Abubakar ya bayyana yadda aka kama wadanda ake zargin a wani otel cikin yankin Nasarawa, kilomita kadan daga Abuja
  • An kama su dumu-dumu da bindigu, harsasai masu linzami, carbin harsasai wadanda aka yi amfani dasu da wadanda ba a riga an yi amfani dasu ba da sauran abubuwan ta'addanci

Abuja - Jami'an 'yan sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) wadanda ke bangaren binciken laifuka na kasa sun kama goma daga cikin kungiyar hatsabiban da ake zarginsu su da yi wa wadanda suke tunanin ba mazauna babban birnin Abuja da jihar Nasarawa bane.

Kara karanta wannan

Wani Gwamnan Ya Sake Rokon 'Yan Bindiga Su Aje Makamai Gwamnatinsa Zata Yafe Masu

Kungiyar 'yan ta'adda
'Yan Sanda Sun Damke Kungiyar 'Yan Ta'adda Dake Addabar Abuja da Nasarawa. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Yayin zagaye da wadanda ake zargin, kwamishinan 'yan sandan FCT, Sadiq Abubakar ya ce an kama wadanda ake zargin ne a otel cikin yankin Masaka na jihar Nasarawa, kilomita kadan daga FCT, jaridar TheCable ta rahoto

Abubuwan da aka gani daga tawagar sun hada da bindiga kirar AK47, bindigu kirar G-3 guda hudu, carbin harsasai guda dari da ashirin da biyu masu girman 6.62mm, bindiga kirar hannu ba tare da harsasanta ba, harsasai masu linzami guda uku, harsasan AK47 wadanda aka yi amfani dasu guda shida da harsasan G-3 guda bakwai da aka yi anfani dasu.

Sauran abubuwa sun hada da layu iri-iri, katin lasisi na 'dan sanda daya, katin 'dan sa kai daya, katin 'dan sandan farin kaya daya, mota kirar Toyota Camry 2000 daya, kalar gwal, mai lamba: GGE 702 CH, mata kirar Gold-3 wagon kalar koriya daya, mai lamba: KWL 22 GQ x, janareto biyu.

Kara karanta wannan

Saboda yawan ganganci: Za a haramtawa 'yan sandan Najeriya shan giya gaba daya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka zalika, 'yan sandan sun yi zagaye da wasu hudu da suka kama dumu-dumu suna fashi da makami a yankin Maitama, Garki, Wuse da tsakiyar birnin tarayyar.

Wadanda ake zargin sun yi fashin ne ga wasu saida kayayyaki da wasu da ake tunanin ba mazauna yankin bane, Channels TV ta rahoto.

Har ila yau, rundunar 'yan sandan Babban Birnin Tarayya wacce ke yaki da garkuwa da mutane yayin aiwatar da ayyukansu sun gano sansannin masu garkuwa da mutane a wajen garin Abuja.

An yi nasarar cafke biyu, inda yayin bincike su fallasa yadda suke samarwa 'yan fashi da 'yan bindiga bindigu.

An gano harsasai masu linzami 900 da sauran abubuwan da ake zargin mallakin wadanda aka yi garkuwa dasu ne.

Hisbah ta tarwatsa motoci 25 na giya a Kano

Kara karanta wannan

Yanzun nan: IGP ya fadi abin da ya kamata a yiwa dan sandan da ya kashe wata lauya mai ciki

A wani labari na daban, hukumar Hisbah ta jihar ta kama wadanda ake zargin 2,260 tare da kwashe almajirai daga tituna.

An gano cewa, jami'an sun tarwatsa motoci 25 na giya a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel