'Yan Bindigan da Suka Sace Ma’aikatan INEC a Kogi Bayan Zabe Gwamna Na Neman Fansa N50m

'Yan Bindigan da Suka Sace Ma’aikatan INEC a Kogi Bayan Zabe Gwamna Na Neman Fansa N50m

  • An ruwaito yadda wasu ‘yan bindiga suka sace jami’an hukumar zabe ta INEC bayan kammala aikin zabe a jihar Kogi
  • 'Yan ta'addan sun bayyana bukatar a ba su zunzurutun kudi har N50m kafin su sako wadanda suka sace
  • Ya zuwa yanzu, ‘yan sanda sun ce sun ceto mutum 96 daga cikin wadanda aka sace, amma an ce akwai saura da yawa

Jihar Kogi - Wadanda suka sace ma’aikatan zabe na INEC a jihar Kogi a zaben gwamna sun nemi a ba su kudin fansa N50m, Arise Tv ta ruwaito.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin a madadin ahalin wadanda aka sacen a Lokoja, Babalola Peter, ya ce ‘yar uwarsa na daga cikin wadanda aka sace a ranar, rahoton Punch.

Idan baku manta ba, an sace wasu daga cikin ma’aikatan zaben gwamna a jihar Kogi a ranar 19 ga watan Maris a Obajana bayan kammala zaben gwamna da ‘yan majalisu a jihar.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wasu 'yan kutse sun shiga jihar Arewa, sun hallaka masunta 4 da magidanci

Ana neman kudin fansan N50m kan jami'an INEC da aka sace a Kogi
Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

An ruwaito cewa, ‘yan ta’adda sun sace jami’an na INEC ne yayin da suke kan hanyar dawowa daga yankunan Kupa ta Arewa da Kudu karamar hukumar Lokoja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ceto mutum 96, inji ‘yan sanda

Sai dai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP William Aya ya shaidawa manema labarai cewa, an ceto mutum 96, inda wasu uku suka jikkata, mutum biyu kuma ana ci gaba da duba su.

A bangarensa, Peter ya bayyana shakku tare da kalubalantar ‘yan sanda kan cewa an ceto dukkan mutanen da tsagerun suka sace.

Muhammad Maimunat da Abdulrahman Raji na daga cikin ‘yan bautar kasa da Peter yace har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutanen.

Sauran mutanen da ke hannun ‘yan ta’adda

Sauran jami’an na INEC da suka saura a hannun masu garkuwa da mutane a cewar Peter sun hada da Oyaniran Atinuke Ruth, Florence Shayo Ajayi, Opara Tina da Blessing.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun harbe jami'an gwamnati na NSCDC 3, a wata jiha

Ya kuma yi bayanin yadda ‘yan ta’addan ke neman makudan kudade kafin su sako wadannan jami’an na INEC da ke hannunsu.

Hakazalika, ya yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su hada kai domin tabbatar da ceto bayin Allah.

An yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Kogi don jin karin bayani, amma bai dauki waya ba sadda aka kira shi.

Har yanzu akwai jihohin da ba a kammala zaben gwamna ba a Najeriya, za a karasa zabukan a ranar 15 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.