Ya Kamata Buhari Ya Zama Shugaban Kwamitin Amintattu Na APC, Sanata Kalu Ya Ba da Shawari
- Orji Kalu, daya daga cikin sanatocin APC a Kudu maso Gabas ya bayyana bukatar damawa da Buhari a shugabancin APC
- Ya ce ya kamata a ba Kudu maso Gabas kujerar shugaban majalisar dattawa a wannan karon mai sarkakiya
- ‘Yan siyasa da yawa na ci gaba da bayyana sha’awarsu ga maye gurbin Ahmad Lawal a shugabancin majalisa
FCT, Abuja - Sanata Orji Kalu ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya karbi kujerar shugaban kwamitin amintattun jam’iyyar APC idan ya mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Ya ba da wannan shawarin ne a wata ganawa da ya yi da shugaban kasa Buhari a gidan gwamnati da ke Abuja a ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.
Kalu ya ziyarci Buhari ne domin sanar dashi manufarsa ta maye gurbin Ahmad Lawal a shugabancin majalisar dattawa.
Dalilin da yasa Buhari ya cancanci rike kujerar
A cewar Kalu, ya kamata a ba yankin Kudu maso Gabas damar rike kujerar shugaban majalisa a wannan karon.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kalu, wanda yace ya tattaunawa da sauran jiga-jigan APC kan batun, ya kara da cewa, jam’iyyar ta fuskanci matsaloli da yawa gabanin zaben shugaban kasa da aka yi.
A fahimtarsa, idan Buhari zai shiga tsakani a lamuran jam’iyyar zai ceto ta daga durkushewa a nan gaba.
Ya kamata a ba Kudu maso Gabas kujerar shugaban majalisar dattawa
Kalu, wanda a yanzu shine babban mai ladabtarwa na majalisar, ya ce ya kamata a duba tare da mika kujerar shugaban majalisar dattawa zuwa yankinsu.
Ya bayyana cewa, duk da yankin bai zabi Tinubu ba, amma ba da kujerar shugaban majalisa ga yankin zai kawo zaman lafiya da mutuntawa a kasar, New Telegraph ta ruwaito.
Ba Kalu kadai bane ya bayyana aniyarsa ta hawa kujerar Ahmad Lawal ba a wannan shekarar, akwai ‘yan siyasa da yawa da suka nuna sha’awarsu daga Kudu da Arewa.
Yari na neman kujerar shugaban majalisar dattawa
A bangare guda, Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana bukatar a ba Arewa maso Yamma shugabancin majalisar dattawa.
A cewarsa, shi ne ya fi cancanta a ba wannan kujerar don jan ragamar majalisar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Baya ga shi, ‘yan Arewa da yawa sun bayyana sha’awarsu na rike wannan kujera mai daraja a Najeriya.
Asali: Legit.ng