Hukumar Zabe Ta INEC Ta Ce Akwai Kura a Zaben Adamawa, Ta Ce Ya Zama ‘Inconclusive’

Hukumar Zabe Ta INEC Ta Ce Akwai Kura a Zaben Adamawa, Ta Ce Ya Zama ‘Inconclusive’

  • Hukumar zabe a jihar Adamawa ta bayyana rashin amincewa da sakamakon zaben da aka tattara a jihar
  • Ta zargi aringizon kuri'u daga yankunan jihar, inda tace an samu kuskuren da dole a warware kafin ayyana mai nasara
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da tattara sakamakon zaben jihohi a Najeriya, ba a kawo na Adamawa ba

Jihar Adamawa - Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta ce akwai kura a sakamakon zaben gwamnan jhar Adamawa, don haka bata amince dashi ba.

Hukumar ta bayyana hakan ne a birnin Yola a cibiyar tattara sakamakon zaben da daren Litinin 20 ga watan Maris.

Ya yi bayanin cewa, an soke zabe a yankuna 47 mai adadin masu kada kuri'u 41,796, wanda ya zarce adadin kuri'u 31,249 da aka kadawa jam'iyyun PDP da APC a zaben na bana.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar APC Ta Ƙara Lallasa PDP, Ya Lashe Zaben Gwamna a Ƙarin Wata Jihar

INEC bata amince da sakamakon zaben Adamawa ba
Yadda zaben Adamawa ya kasance | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hakazalika, an ce Aisha Binani ta jam'iyyar APC ta samu kur'u 390,275 yayin da gwamna mai ci, Ahmadu Finitiri ya samu kuri'u 421,524 a zaben na bana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Cikakken sakamakon da aka sanar

Adadin masu akda kuri'un Adamawa - 2,196,566

Adadin masu akda kuri'un da aka tantance - 859, 964

Sakamakon zabe daga jam'iyyu daban-daban

AA. 641

ADC 2,996

ADP 2,13,4

APC. 390,275

APGA 876

APM. 603

Kara karanta wannan

Zaben Gwamna: Hukumar INEC Ta Sanar da ‘Inconclusive’ a Kebbi

APP 284

LP 2729

NNPP. 4847

NRM 1,237

PDP 421,524

PRP. 1185

SDP. 6,865

YPP. 1,425

ZLP. 199

Sahihan kuri'u 837,820

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC Ya Sha Da Ƙyar, Ya Lashe Zaben Gwamna a Jiharsa

Kuri'un da suka lalace 14,888

Kadadin kuri'un da aka kada 852,748

An sace masu kai sakamakon zaben jihar Zamfara

A wani labarin kuma, kunji yadda aka sace wasu jami'an hukumar zabe ta INEC da ke kan hanyarsu ta zuwa Gusau daga Maradun don kai sakamakon zaben gwamna.

An ruwaito cewa, ana ci gaba da samun tsaiko ga zaben gwamnan da aka yi a jihar a karshen makon jiya, har yanzu ba a sanar da wanda ya lashe zaben ba.

Sai dai, an ce an sako jami'an, duk da ba a bayyana yadda aka yi suka kubuta ba daga sacesu da aka i ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel