Muhimman Abubuwa 7 Game Da Tsohon Hafsan Hafsoshin Soji Na Zamanin Abacha, Laftanar Janar Diya

Muhimman Abubuwa 7 Game Da Tsohon Hafsan Hafsoshin Soji Na Zamanin Abacha, Laftanar Janar Diya

Tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin mulkin soja, Oladipo Diya, ya rasu. Diya shi ne mataimakin tsohon shugaban mulkin soja, Sani Abacha, ya rasu ya na da shekaru 78.

Da ya kara kwanaki kadan, zai cika shekara 79 ranar 3 ga watan Afrilu.

Dipo Diya
Abubuwa 7 masu muhimmanci game da marigayi Oladipo Diya. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

A wata sanarwa da Barista Oyesinmilola Diya ta fitar, a madadin iyalansa, ta tabbatar da mutuwar tsohon shugaban ma'aikatan tsaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce Diya ya rasu da safiyar Lahadi.

''A madadin gaba daya iyalan Diya da ke gida da ketare; mu na sanar da rasuwar Miji, Uba, Kaka, Dan uwa, Laftanar Janar Donaldson Oyeyinka Diya (mai ritaya) GCON, LLB, BL, PSC, FSS, mni.
''Mahaifinmu ya rasu da safiyar 26 ga watan Maris 2023.

Kara karanta wannan

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban Mataimakin Shugaban Kasa Ya Mutu

''Mu na rokon addu'o'inku a wannan lokacin da mu ke cigaba da jimamin mutuwarsa. Za a sanar da halin da ake ciki nan gaba kadan,'' kamar yadda sanarwar ta shaida.

Bisa hakan muka kawo muku wasu muhimman abubuwa game da Diya kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ga wasu abubuwa 7 da ya kamata a sani game da marigayi Dipo Diya

1. An haife shi ranar Litinin, 3 ga watan Afrilu, 1944 a Odogbulu, da ke Jihar Ogun, lokacin ta na shiyyar yamma, Najeriya.

2. Diya ya halacci makarantar Yaba Methodist School, Lagos daga 1950-1956 daga ya cigaba da karatu a garinsu, Odogbulu, a matsayin dalibin Odogbulu Grammar School, daga 1957-1962.

3. Ya shiga makarantar horon soji ta Nigerian Defence Academy, Kaduna ya kuma yi yaki lokacin lokacin yakin basasa a Najeriya.

An nada shi mukamin Second lieutenant a watan Maris din 1967. Daga nan ya tafi US Army School of Infantry, Command and Staff College, Jaji (1980-1981) sannan ya wuce zuwa National Institute for Policy and Strategic Studies, Kuru.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Ceto Mutum 201 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Borno Da Kaduna

Ya na aikin soja, Diya ya karanci ilimin shari'a a jami'ar Ahmadu Bello, da ke Zaria, in da ya samu digiri na farko a fannin shari'a, ya kuma wuce makarantar horar da daliban shari'a, in da ya zama cikakken lauya.

4. Ya zama babban jami'in shiyya ta 82, a rundunar sojiin Najeriya a 1985 sannan ya zama kwamandan National War College (1991-1993)

5. Shi ne tsohon shugaban ma'aikata a mulkin soja, wanda ke zaman mataiki ga shugaban soja, Sani Abacha.

6. A 1997 Diya da wasu gamayyar sojiji an yi zargin sun shiryawa gwamnatin Sani Abacha juyin mulki. Juyin mulkin da wasu ma su biyayya ga Sani Abacha su ka hambarar, kuma aka daure Diya da abokan aikinsa a gidan yari.

An gurfanar da Diya a gaban kotun sojoji aka kuma yanke masa hukuncin kisa. Bayan mutuwar Abacha a 1998, shugaban soji na wancan lokacin, Abudusalami Abubakar ya yafewa Diya.

Kara karanta wannan

Saura Watanni 2 Ya Bar Ofis, Buhari Ya Karfafi Muhimmin Aikin da Ya Tattago a Arewa

7. Shi ne gwamnan soji na Jihar Ogun daga watan Janairu 1984 zuwa watan Augusta na 1985.

Abdullahi Abacha, dan marigayi Janar Sani Abacha ya riga mu gidan gaskiya

A wani rahoton daban, kun ji cewa Abdullahi Abacha, dan marigayi shugaban kasa na zamanin soja, Janar Sani Abacha ya riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni sun ce marigayin ya rasu cikin barcinsa a gidansu da ke birnin tarayya Abuja a layin Nelson Mandela.

Asali: Legit.ng

Online view pixel