Sauran Ƙiris In Haƙura Da Karatu Ina Aji 3 Na Firamari, In Ji Goodluck Jonathan
- Shugaba Jonathan ya bayyana yadda ya kusa barin karatu tun ya na aji uku a firamare ba don taimakon kawunsa ba
- Jonathan ya bayyana haka ne a wajen jana'izar kanin mahaifiyarsa da ya taimaka ma sa ya cigaba da karatu
- Jonathan ya bayyana kawunsa a matsayin mutumin kirki, da ya zama abin koyi ga kowa a iyalai da sauran al'umma
Bayelsa - Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi magana kan irin kalubalen da ya fuskanta lokacin ya na dalibin makarantar firamare, yana cewa ya kusa hakura da makarantar ba don taimakon kawunsa ba, marigayi Omieworio Afeni.
Omieworio Afeni, kanin mahaifiyar Jonathan, Eunice, wanda ya rasu ya na da shekara 87 an binne shi ranar Alhamis a Otuoke, da ke karamar hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa bayan kammala bikin binniya na al'adar kirista a cocin Angalika ta St. Stephen, da ke Otuoke.
Kawu na ne dalilin da yasa na yi nasara a karatu, Jonathan
Da ya ke jawabi lokacin jana'izar, tsohon shugaban Najeriya ya ce kawunsa ne silar nasarar karatun da ya yi, ya na mai cewa shi ya tsaya ma sa ya cigaba da karatu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana marigayin kawunsa a matsayin mutum mai nuna kulawa wanda ya san ya kamata.
Ya ce:
''Kawuna mutum ne mai kulawa sosai. Da tuni na hakura da karatu tun ina aji uku a firamare, amma kawu ya tsaya min don cigaba da karatu.
''A matsayin mu na kiristoci, wakilai ne mu a bayan kasa, an raba mana hakkoki da dama yayin da mu ke raye a duniyar da mutuwa ta zama dole, matukar lokacin mu ya yi.
''Duk da yarda da haka da kowanne mai rai ya yi, akwai radadi da mutuwa ke zuwa da shi musumman ga wanda mu ke kauna, duk kuwa da yanayin da mutuwar ta zo ku a shekarun da aka mutu."
Ya cgaba da cewa:
''Za mu cigaba da kewar wanda mu ke kauna saboda tarihin da ke tsakaninmu, lokacin da mu ka shafe tare, tarihin da su ka bari, da kuma darasin da mu ka koya daga lokacin rayuwarsu zuwa mutuwarsu.
''Irin wannan yanayin shi na ke ciki a yanzu na rashin, wanda na ke addu'ar nema ma sa gafara, kawuna abin kaunata, Omieworio Afeni, wanda ya rayu shekaru 87.
''Kawuna mutumin kirki ne, mai sanin ya kamata, mai tarbiya, mai gaskiya, kuma mai taimakon zuri'a da duk wanda ya rabe shi.
''Mutum ne mai son zumunci, abin kaunar mahaifiyata, wanda ya zama matsayin uba tun ya na dan karami, ya kuma rayu a matsayin abin koyi ga sauran iyalansa da al'umma.''
Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bayyana mutuwa a matsayin makomar kowacce rai, ya na mai rokon yan Bayelsa su kasance ma su kaunar juna.
Ya ce marigayi Afeni, ya rayuwa cikin aminci da ya cancanci yabo, inda shugaba Jonathan ya samo kyawawan halayensa.
An yi rikici tsakanin wakilan jam'iyyar APC da PDP a Ogun
Wakilan jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP da na All Progressives Congress, APC, sun yi rikici a ranar Lahadi 19 ga watan Maris a cibiyar tattaro kuri'u zaben gwamnan jihar Ogun na 2023.
Asali: Legit.ng