Ramadan: Atiku Ya Ba ’Yan Najeriya Sako Mai Daukar Hankali, Ya Bukaci Sanya Kasa a Addu’a

Ramadan: Atiku Ya Ba ’Yan Najeriya Sako Mai Daukar Hankali, Ya Bukaci Sanya Kasa a Addu’a

  • An bukaci Musulman Najeriya a cikin watan Ramadana na bana da su yi sadaukarwa ga kasar don ci gabanta
  • Tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ne ya yi wannan kiran a sakon da ya aikawa Musulmai yayin da watan mai alfarma ya shigo
  • Ya kuma yi kira ga ‘yan kasar da su dukufa da yiwa Najeriya addu’ar waraka daga dukkan cututtukan da ke cikinta

FCT, Abuja Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bukaci Musulmai da su yiwa kasar addu’a a cikin watan Ramadana mai alfarma.

Wannan na fitowa ne daga cikin wata sanarwar da Atiku ya fitar a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris, inda yace kasar na cikin rudani da ke bukatar addu’a.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu riko da zaman lafiya tare da yin duk wata sadaukarwa da za su iya a watan don warakar Najeriya.

Kara karanta wannan

Za ku sha mamaki: Sabon gwamnan wata jiha ya fadi yadda zai ji da albashin ma'aikata a jihar

Atiku ya tura sako ga Musulman Najeriya
Tsohon mataimakin shugaban kasa a Najeriya, Atiku Abubakar | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Duk Musulmi ya san fa’idar watan Ramadana

A cewar sanarwar da ya fitar da TheCable ta samo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“A matsayinmu na Musulmai, muna da fahimtar cewa abin da ake so a wannan watan mai alfarma shine sadaukarwa da kankan da kai ga Allah.
"A matsayinmu na ‘yan Najeriya, Ramadana na wannan shekarar ya zo a daidai lokacin da kasarmu ke cikin sarkakiya."

A cewarsa, ‘yan Najeriya kowa na cikin rundani da dar-dar, inda yace ya kamata a yi amfani da wannan watan a matsayin damar rokon Allah ya warware dukkan matsalolin kasar.

Ya kara da cewa, daya daga fa’idojin watan shine samun damar Musulmi ya warkar da zuciya daga matsaloli, don haka Najeriya na bukatar addu’ar duk wani Musulmi.

Atiku ya sha kaye, yana kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na bana

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, Atiku na ci gaba da tattara hanyoyin da zai kalubalanci dan zababben shugaban kasa a Najeriya na APC, Bola Tinubu a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Sanatan Jihar Kano Ya Shiga Sahun Masu Neman Kujerar Majalisar Dattawa a 2023

An sanar da sakamakon zaben shugaban kasa, inda aka ce Tinubu ya lashe zaben da kuri’un da suka fi na Atiku a zaben 25 ga watan Faburairu.

Ya zuwa yanzu, an ba Atiku damar duba kayan aikin da aka yi amfani dasu a zaben bana don sanin inda aka samu matsala.

Kafin Atiku, sarkin Musulmi na Najeriya ya taya Musulmai murnar shigowar Ramadana, inda ya bukaci a yiwa Najeriya addu’o’in alheri da ci gaba cikin watan mai alfarma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel