Yadda Gemu Ya Fitowa Wata Kyakkyawar Budurwa, Mijinta Ya Rabu Da Ita

Yadda Gemu Ya Fitowa Wata Kyakkyawar Budurwa, Mijinta Ya Rabu Da Ita

  • Mandeep Kaur ta yi aure a 2012 kuma tana ganin ta samu abokin rayuwa duk rintsi duk wuya
  • Mijin Kaur ya gudu ya barta a lokacin da ta fara samun gemu suna fito mata a fuska, wanda haka ya sa ta zama kamar namiji
  • Matashiyar mai shekaru 33 ta shiga yanayi bayan mutuwar aurenta, tana ganin ta kare mata babu wani abun duba a gaba

Mijin Mandeep Kaur ya rabu da ita yan shekaru bayan aurensu sakamakon gemu da ya fara fito mata a fuska.

Matashiya mai dauke da gemu a fuska
Yadda Gemu Ya Fitowa Wata Kyakkyawar Budurwa, Mijinta Ya Rabu Da Ita Hoto: News
Asali: UGC

Kaur ta shiga wani yanayi bayaj mijinta wanda take kallo a matsayin sahibin ranta ya rabu da ita saboda gemun da ya fitar mata a fuska.

Menene halittar ‘hirsutism’?

A cewar Mayo Clinic, ‘hirsutism’ wani yanayi ne a jikin mata wanda ke sa gashi mai yawa ya fitar masu a fuska, kirji da baya kamar maza.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Aka Sa Amarya Tuka Tuwo a Taron Bikinta Ya Bar Mutane Baki Bude

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

News ta rahoto cewa Kaur tana ganin an nuna ba’a kaunarta amma sai ta nemi taimako. Matashiyar mai shekaru 33 ta fara zuwa Gurfwara- wajen bauta tsakanin Sikhs.

Yarda da kai

A hankali, Kaur ta fara yarda da yanayin halittarta, sannan ta fara ajiye gemunta. Ta fara sanya rawani sannan bata aske gemun nata da gashin baki.

Ta koma tuka babur a fadin kauyenta sannan tana zuwa gona tare da yan uwanta maza. Wasu na yi mata kallon namiji amma yanayin maganarta na fito da jinsinta na mace.

Ta ce ta dauki lokaci sosai kafin ta yarda da kanta a yadda Allah ya yi ta, don haka ta daina jin kunyar gemunta.

Budurwa ta shiga dimuwa bayan mahaifiyarta ta karanta hirarta da saurayinta a waya

A wani labari na daban, wata budurwa ta shiga tashin hankali matuka bayan mahaifiyarta ta yi mata kutse a yanayin rayuwar da take yi a wayarta a boye.

Kara karanta wannan

“Na San Yadda Yake Ji": Budurwa Ta Jizga Saurayinta a Bainar Jama’a, Ta Karbe Wayar Da Ta Siya Masa a Bidiyo

Mahaifiyar yarinyar dai ta dauki wayarta sannan ta bude manhajar Whatsappa da ke kan wayar inda ta dunga bin hirarrakinta da saurayinta daya bayan daya tana karantawa.

Wannan al'amari ya jefa yarinyar cikin halin fargaba yayin da ta yi zuru tana kallon talbijin da ke fallon amma a zahirin gaskiya bata fahimtar komai daga abun da ake yi a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel