Gwamnati Ta Gurfanar da Tukur Mamu, DSS Za Ta Cigaba da Rike 'Mai Sulhu da ‘Yan Ta'adda
- Da alama gwamnatin tarayya ta kammala wasu shirye-shirye domin gurfanar da Tukur Mamu
- Za ayi karar Mamu a babban kotun tarayya mai zama a birnin Abuja watanni da cafke shi
- Babban lauyan gwamnatin tarayya yana tuhumar wannan mutumi da laifuffukan ta’addanci
A yau gwamnatin tarayya za ta gurfanar da Tukur Mamu a gaban kotu, bisa wasu zargi da su ke da alaka da laifin ta’addanci.
Hukumar dillacin labarai ta ce za ayi karar Malam Tukur Mamu a kan zargin laifuffuka goma a kotun tarayya da yake Abuja.
Ofishin Ministan shari’a kuma babban Lauyan gwamnati zai kai Mamu gaban Alkali Inyang Ekwo a madadin gwamnatin tarayya.
NAN ta ce kafin yanzu Mai shari’a Nkeonye Maha ya ba jami’an DSS dama su tsare wannan mutumi na tsawon kwanaki 60.
Wannan zai ba hukumar tsaron dama ta kammala duk wasu bincike a kan wanda ake zargi yana da alaka da miyagun ‘yan ta’adda.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jirgin Kaduna-Abuja
Hakan na zuwa ne bayan an tuhumi Mamu da hannu wajen sakin wasu daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a jirgin kasa.
Darektan gurfanar da jama’a na gwamnatin tarayya, M.B. Abubakar ya sa hannu a takardar karar da ake sa ran a fara saurara yau.
Jaridar nan ta Daily Nigerian ta fitar da irin wannan labari a safiyar Talata.
DSS za ta rike Mamu
The Nation ta ce an gurfanar da Mamu ne shi kadai, kuma da aka karanto masa zargin da ke wuyansa, ya amsa da cewa ba aikata su ba.
Lauyan wanda ake kara, Mohammed Katu (SAN) ya nemi kotu ta bada belinsa.
Aderonke Imana wanda ta tsayawa gwamnati a shari'ar ta ce babu dalilin bada beli domin larurar Mamu ba ta fi karfin jami'an DSS ba.
Mai shari'a Inyang Ekwo ya saurari kowane bangare, ya kuma gamsu DSS ta cigaba da rike 'dan jaridar har sai an kai ga yanke hukunci.
Ta'addancin zabe a Ribas
A baya an samu rahoton kashe shugaban kwamitin neman takarar jam'iyyar APC na karamar hukumar Ahoada ta yamma a jihar Ribas.
An harbi Chisom Lennard ne a lokacin da yake kokarin hana wasu miyagu satar kayan zabe a mazabarsa, dalibi ne a jami'ar Jiha.
Asali: Legit.ng