Badakalar N40m: Jarumar Kannywood, Amal Umar Ta Roki Kotu Da Ta Hana Yan Sanda Kama Ta

Badakalar N40m: Jarumar Kannywood, Amal Umar Ta Roki Kotu Da Ta Hana Yan Sanda Kama Ta

  • Jarumar fim Amal Umar ta garzaya kotu kan zarginta da ake da damfarar kudi naira miliyan 40
  • Shahararriyar yar Kannywood din ta roki kotu ta hana yan sanda kama ta da kuma bincikenta
  • Wani dan kasuwa ne ya maka jarumar a kotu kan zargin cewa ta damfare shi naira miliyan 40 da sunan za su bude shagon waya

Kano - Fitacciyar jarumar Kannywood, Amal Umar, ta tunkari babbar kotun tarayya da ke Kano inda ta nemi da ta hana kwamishinan yan sandan jihar Kano kama ta.

Jaruma Amal dai na fuskantar zargi na damfarar wasu kudade da yawansu ya kai naira miliyan 40, rahoton Daily Trust.

Jarumar kannywood Amal Umar dauke da murmushi
Badakalar N40m: Jarumar Kannywood, Amal Umar Ta Roki Kotu Da Ta Hana Yan Sanda Kama Ta
Asali: Facebook

A shekarar da ta gabata ne rundunar yan sandan jihar Kano ta kaddamar da bincike kan jarumar bisa zarginta da hada kai da wani Ramadan, wanda ake zargin saurayinta ne wajen damfarar wani dan kasuwa, Alhaji Yusuf Adamu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bindige Tsohon Kansila A Kano Har Lahira Kan Sace Akwatin Zabe

Dan kasuwar ya zarge ta da karbar masa kudi tare da yarjejeniyar cewa za su kafa wani kasuwanci na siyar da waya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, jarumar ta gaggauta zuwa kotu karkashin jagorancin Sunusi Ado Magaji, wanda ya dage sauraron shari'ar zuwa watan nan.

Yadda ta kaya a kotu bayan dawo da zama kan shari'ar

Da kotu ta dawo zama kan lamarin a ranar Juma'a, lauyan gwamnati, Barista Badamasi, ya gabatar da takardu da ke nuna yadda jarumar ta damfari mutumin kudi naira miliyan 40.

Sai dai kuma, Amal Umar, ta hannun lauyanta, Barista Adama Usman, ta ce mai karan ya bata naira miliyan 8 don ta bude shago sannan ya bata naira miliyan 3 don ta biyawa mahaifinta bashi. Ta kuma gabatar da takardu don kare jawabinta.

Marista Adama, ta bukaci kotu da ta hana yan sanda yin bincike tare da yunkurin kama wacce take karewa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gobara Ta Sake Tashi A Wata Babban Kasuwar Borno, Hotuna Sun Fito

Daily Trust ta rahoto cewa Mai shari'a Magaji ya dage shari'ar zuwa 17 ga watan Afrilun 2023.

A wani labari na daban, wata matashiya mai suna Mandeep Kaur ta shiga damuwa da karayar zuciya bayan mijinta ya gudu ya barta saboda gemu sun fito mata a fuska sannan hakan ya sa ta koma tamkar wata namiji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng