Jami'in Tattara Sakamakon Zabe A Kano Ya Yanke Jiki Ya Fadi A Hedkwatar INEC

Jami'in Tattara Sakamakon Zabe A Kano Ya Yanke Jiki Ya Fadi A Hedkwatar INEC

  • An shiga dimuwa a hedikwatar hukumar zabe mai zaman kanta INEC a ranar Lahadi yayin da baturen zabe na karamar hukumar Kura a Kano ya yanke jiki ya fadi
  • Farfesa Muhammad Yushau ya fadi ne a kofar shiga hukumar zaben domin ya gabatar da kuri'u da aka tattaro daga rumfunan zabe da ke karamar hukumar da ke karkashin kulawarsa
  • Takwararsa na Garun Malam, Muhammad Shuaibu Abubakar wanda suka taho a mota guda shine ya gabatar da sakamakon a madadinsu bayan amincewar dukkan jam'iyyun siyasa da suka fafata a takarar

Jihar Kano - Jami'in tattara sakamakon zabe na karamar hukumar Kura da ke jihar Kano, Farfesa Muhammad Yushau ya yanke jiki ya fadi a kofar shiga a hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta na kasa INEC, a Kano.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sun Kama Shahararren Dan Majalisar Kano Kan Yunkurin Kona Ofishin INEC

An garzaya da shi wani asibiti da ba a bayyana suna ba an kwantar da shi kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Takarar
Jami'in Tattara Sakamakon Zabe A Kano Ya Yanke Jiki Ya Fadi A Hedkwatar INEC. Hoto: The Cable
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takwararsa daga Garun Malam, Muhammad Shuaibu Abubakar, wanda suka taho cikin mota guda ya ce zai gabatar da sakamakon zaben a madadinsa, da taimakon jami'in zabe, Maryam Adamu Abdullahi daga karamar hukumar Kura.

Dukkan jam'iyyun siyasa sun yarda da wannan tsarin saboda faruwar lamarin da ba a yi tsammani ba.

Masu zabe sun ki karbar tiransifa ta kudi a jihar Neja yayin zaben gwamnoni da yan majalisun jiha

Wasu cikin wadanda suka tafi kada kuri'arsu a karamar hukumar Tafa ta jihar Neja sun ki yarda da alkawarin tiransifa da aka musu daga wakilan jam'iyyu suka ce sun gwammace a ba su abinci kafin su yi zaben a ranar Asabar da ta gabata.

Kara karanta wannan

An kuma: Hukumar INEC ta ayyana zaben wani yankin Kano 'Inconclusive'

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, wasu cikin masu zaben sun ce an musu irin wannan alkawarin na tiransifa a baya yayin zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu amma ba a cika musu ba.

Wata cikin wadanda suka yi zaben da ta ce sunanta Angela, ta ce suna sane cewa abin da suka aikata laifi ne karkashin dokar kasa kuma amma dai hakan ne hanya guda da za su iya morar yan siyasan domin ba za su sake ganinsu ba sai wani zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel