Sojoji Sun Yi Wa Dan Majalisar Tarayya Dukan Tsiya Tsakar Dare A Otel Dinsa

Sojoji Sun Yi Wa Dan Majalisar Tarayya Dukan Tsiya Tsakar Dare A Otel Dinsa

  • Dan majalisar tarayya mai wakiltar Baruku, da ke Jihar Benue, Kpam Sopu ya sha dukan tsiya a hannun sojoji
  • Sokpo ya bayyana cewa bai san dalilin da ya sanya su ka aikata masa haka ba, yayin da ya ke asibiti ya na karbar magani
  • Hukumomin soji da yan sanda sun ce ba su da masaniyar faruwar lamarin, amma za su yi bincike

Jihar Benue - Dan majalisa tarayya mai wakiltar mazabar Buruku, Kpam Sokpo, ya sha dukan tsiya a hannun sojoji na musumman da ke bataliya ta 401 a Jihar Benue, rahoton Daily Trust.

An ruwaito cewa Sokpo ya sha dukan a Old Barn a da ke garin Gboko, karamar hukumar Gboko da ke jihar lokacin da sojojin su ka isa masaukinsa da misalin 2:30 na dare.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Mutum 3 Sun Mutu a Wani Mummunan Hatsari Da Ya Cika da Ayarin Gwamnan Katsina

Dan Majalisar Tarayya, Sokpo
Sojoji sun yi wa dan majalisar tarayya duka a Jihar Benue. Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Yadda abin ya faru

Dan majilasar tarayyar wanda ya shaida wa wakilin majiyarmu yadda lamarin ya faru ta waya, ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

''Ban san me ya faru da su ba, na dawo masaukina a otal din da na ke a Gboko, Old Barn da misalin 2:30 na dare lokacin da tankar sojoji cike da sojoji sama da 60 su zo.
''Ina zaune da wasu abokaina. Lokacin da su ka sauko daga motocinsu, kowa ya samu wajen tsayuwa. Na tashi daga inda na ke don in yi wani abu sai daya daga cikinsu ya tunkare ni ya na tambayata me yasa na ke tafiya yadda na ke tafiya.
''Ina cikin magana, sai ya kwada min mari a fuska. Na tambaye shi me yasa ya yi min haka tare da gabatar da kai na a matsayin dan majalisar tarayya. Na fada ma sa bai sanni ba kawai zai mari fuskata? Kafin in ankara, sama da 30 daga cikinsu su ka rufar min da duka da kasan bindiga don su yi min rauni."

Kara karanta wannan

Mota Dauke Da Yara Yan Makarantar Firamari Ta Yi Kundunbala A Legas

Ya cigaba da cewa:

''Maganar da na ke maka yanzu akwai dinki a fuska ta, da kaina kuma naji ciwo a jikina gaba daya. Ana cikin haka, kwamandansu ya dakatar da su. Daga baya, sun ka cigaba da cin zarafina ta re da karbe komai da ke cikin mota ta ba su bar koda takarda ba.
''Wanda ya fara yi min wannan cin mutunci ya na barazanar za su iya kashe ni. Ban ga sunan ko daya ba saboda sun cire sunayensu kafin su ci zarafina.
''Ka yarda da ni, bansan dalilin da ya sa su ka min haka ba. Na je asibiti don a dinke inda na yanke da kuma yin magani, amma na shigar da rahoto ga yan sanda da kuma mai bawa gwamna shawara kan harkokin tsaro na Jihar Benue.''

Martanin Sojoji

Da aka tuntubi mai magana da yawun bataliyar sojoji na musamman ta 401, Kaftin Okeize, ya ce zai yi bincike don sanin hakikanin abin da ya faru, ya kara da cewa bai samu rahoto kan lamarin ba.

Kara karanta wannan

2023: Jonathan Ya Ba Wa Yan Siyasa Shawara Mai Ratsa Jiki Ana Daf Da Zaben Gwamnoni

Shi ma, kwamishinan yan sandan jihar, Abbas Wale, ya ce bai san da faruwar al'amarin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel