Ma’aikatan INEC Sun Yi Zanga-Zangar Rashin Biyansu Kudaden Alawus a Jihar Bauchi
- Rahoto daga jihar Bauchi ya bayyana yadda aka kai ruwa rana da wasu ma'aikatan wucin gadi da hukumar zabe ta INEC ta dauka a zaben bana
- A cewar majiya, ma'aikatan sun yi turjiya bisa rashin biyansu hakkinsu, inda suka yi zanga-zangar nuna adawa da hakan
- Bayan shawo kan lamarin, an ce sun ci gaba da aikinsu na ji da zaben gwamna da 'yan majalisun jiha a jihar ta Bauchi
Jihar Bauchi - Wasu ma’aikatan wucin gadi na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) sun yi zanga-zangar rashin biyansu hakkinsu na aikin zabe a ranar Asabar.
Wannan lamarin ya jawo jinkiri fara aikin zaben gwamnoni da ke aka tsara a kamarar hukumar Bauchi ta jihar Bauchi.
Duk da karbar kayayyakin aikin zaben, ma’aikatan sun ki su bar cibiyar tattara sakamakon zabe ta Baba-Sidi a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Amma a lokacin da wani babban jami’in hukumar INEC ya sa baki, ma’aikatan na wucin gadi sun tafi bakin aiki da misalin karfe 9:15 na safe.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yadda bidiyo ya nuna kwamishinan Bauchi na raba kudi a bainar jama'a
A wani bidiyon da aka yada, an ga lokacin da kwamishina matasa da wasanni na jihar Bauchi ke raba kudi ga jama'a a jihar.
Wannan ya faru ne a jajiberin zabe, inda yake bayyana bukatar a zabi jam'iyyar PDP mai mulkin jihar a yau Asabar.
An ga jami'an 'yan sanda na zagaye dashi a lokacin da yake aikata wannan aikin da ya saba da dokar zabe ta Najeriya
An sayen kuri'u, kana a rantse a jihar Neja
A wani labarin na daban, kunji yadda wasu bata-gari ke sayen kuri'un talakawa da kayan abinci a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya a zaben gwamna na bana.
Rahoto ya bayyana cewa, ana sayen kuri'un ne da taliya, yadi, bokiti da Maggi, lamarin da ya dauki hankalin jama'a da yawa a jihar.
Hakazalika, an ce akan nemi mata su rantse za su zabi wasu 'yan takara kafin a dauki ledar taliya a basu a wannan zaben da aka yi yau Asabar.
Asali: Legit.ng