Na’urorin Tantance Masu Kada Kuri’u Na BVAS Guda 22 Sun Bata a Jihar Ribas
- Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana yadda na’urorin BVAS suka bata gabanin zaben gwamnoni
- Wannan lamarin ya faru ne a jihar Ribas da ke Kudancin Najeriya, lamarin da ya ja hankalin YIAGA Afrika
- Ya zuwa yanzu, hukumar ta ce batan na’urorin ba zai shafi zaben da ke tafiya ba a halin yanzu a Najeriya
Jihar Ribas - Akalla na’urorin BVAS na tantance masu kada kuri’u guda 22 ne suka yi batan-dabo a zaben gwamna da ‘yan majalisun jiha a Ribas, TheCable ta ruwaito.
An ruwaito cewa, an kai na’urorin BVAS sama da 6865 jihar gabanin zaben yau Asabar bayan da aka tabbatar da ingancinsu.
An tattaro cewa, wasu na’urori uku na BVAS sun lalace ta yadda ba za a iya gyara su, don haka ba a kawo su wurin kada kuri’u ba.
Kwamishinan zaben jihar, Johnson Alalibo ya shaidawa manema labarai da wakilan zabe cewa, hakan ba zai shafi zaben da za a gudanar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Batan BVAS ba zai shafi zabe ba, inji INEC
Alalibo ya ce, hukumar ta shirya yadda za ta maye gurbin duk abin da ya lalace, inda ya kara da cewa, wadanda suka batan ba za su kawo tsaiko ga zaben ba.
Ya shaida cewa, hukumar INEC za ta tabbatar dukkan na’urorin da suka batan ‘yan ta’adda da mabarnata basu yi amfani dasu ba, SaharaReporters ta ruwaito.
Ya kuma yi alkawarin cewa, za a daura sakamakon zabe a kafar yanar gizon da INEC ta tanada ba tare da bata lokaci ba don tabbatar da gaskiya a zaben.
Sai dai, wakilin YIAGA Afrika a jihar, Obinna Ebogidi ya bukaci INEC ta tabbatar da ta cika dukkan alkawuran da ta dauka game da ingancin na’urorin na BVAS.
An ba INEC damar gyara na’urorin BVAS
A wani labarin, kun ji yadda hukumar zabe ta samu sahhalewar kotun daukaka kara game da gyara ga na’urorin tantance masu akda kuri’u na BVAS gabanin zaben gwamnoni.
A cewar alkalan kotu, ba hukumar INEC wannan dama zai taimaka wajen tabbatar da yin zaben gwamnoni cikin tsakani ba tare da wata matsala ba.
Daga baya, an dage yin zaben gwamnoni a Najeriya zuwa ranar 18 ga watan Maris bisa gyare-gyare da ake yi.
Asali: Legit.ng