A dakatar da shi: Hadimin Tinubu Ya Bukaci Buhari Ya Dauki Mataki Kan Gwamnan CBN
- Bayo Onanuga yana ganin babu dalilin da Godwin Emefiele zai cigaba da zama Gwamnan CBN
- Darektan yada labarai na kwamitin takarar Bola Tinubu a 2023 ya na so a sauke Godwin Emefiele
- Tun da kotu ta yi umarni ayi watsi da canjin kudi, Onanuga ya ce Shugaban kasa ya kori Gwamnan
Abuja - Duk da bankin CBN ya yi umarni ga sauran bankunan kasuwa da su rika aiki da tsofaffin kudi, har yanzu kujerar Godwin Emefiele ta na lilo.
Rahotanni sun zo daga New Telegraph cewa Darektan yada labarai da hulda da jama’a na kwamitin zaben APC ya ce a hukunta Gwamnan CBN.
Bayo Onanuga ya fito ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya dakatar da Godwin Emefiele daga kujerar da yake kai tun watan Yunin 2014.
Ganin yadda mutane suke shan wahala har yanzu saboda karancin Naira, Bayo Onanuga ya yi amfani da Twitter, yana mai kira ga shugaban kasa.
An zo da tsarin mugunta
Hadimin na Asiwaju Bola Tinubu yake cewa bai dace Emefiele ya cigaba da rike muhimmiyar kujera a Najeriya irinta Gwamnan babban banki ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto Onanuga yana cewa yunkurin takaita yawon kudi da CBN ya fito da shi mugunta ce.
Tsohon shugaban na hukumar dillacin labarai na kasa ya yi magana da manyan bakake, ya ce akwai bukatar babban bankin ya bar hannun Emefiele.
Maganar Bayo Onanuga
“Ina mamakin yadda Godwin Emefiele yake cigaba da zama a ofishinsa, babu wata nadama, bayan an tilasta masa watsi da mugun tsarinsa na takaita yawon kudi.
Shugaban kasa Buhari ya dakatar da shi daga aiki. Ya kamata Emefiele ya tattara ya tafi YANZU.”
- Bayo Onanuga
Buhari ya yi magana?
Duk da wannan kira da ya fito daga bangaren Bola Tinubu mai shirin zama shugaban Najeriya a watan Mayu, ba ji Muhammadu Buhari ya ce uffan ba.
An dade ana kira da a canza gwamnan CBN, a karshe ma sai dai aka kara masa wa’adi a 2019. Akwai yiwuwar zai bar ofis ne a watan Yunin 2023.
Canjin kudi ya jawo asara - Darektan CPPE
Rahoto ya zo cewa Darektan CPPE a Najeriya ya nuna cewa mutane su na wayyo Allah a dalilin canza N200, N500 da N1000 da aka yi a karshen bara.
Shugaban CPPE, Dr. Muda Yusuf ya ce Naira Tiriliyan 20 aka rasa da bankin CBN ya janye fiye da 70% na kudin da ake da su, sannan an rasa aikin yi.
Asali: Legit.ng