Mace Ta Farko Da Ta Zama Sanata a Najeriya, Franca Afegbua, Ta Mutu

Mace Ta Farko Da Ta Zama Sanata a Najeriya, Franca Afegbua, Ta Mutu

  • Allah ya yi wa mace ta farko da ta hau kujerar Sanata a tarayyan Najeriya, Sanata, Mista Franca Afegbua, ta riga mu gidan gaskiya ranar Lahadin nan 12 ga watan Maris
  • Iyalan gidan marigayyar ne suka tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da su ka fitar a jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya
  • Sanarwan ta ce marigayyar ta yi bakin kokarinta lokacin da take a raye, iyalai zasu sanar da lokacin birne Sanatan

Edo - Mace ta farko da ta zama Sanata a tarihin Najeriya, Sanata Franca Afegbua, ta riga mu gidan gaskiya. Ta mutu ne ranar Lahadi (yau) 12 ga watan Maris, 2023.

Iyalan gidan marigayyar ne suka tabbatar da mutuwar 'yar uwarsu a wata sanarwa da suka fitar a jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bago VS Kantigi: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Manyan Yan Takara 2 a Jihar Neja

Sanata Franca Afegbua.
Mace Ta Farko Da Ta Zama Sanata a Najeriya, Franca Afegbua Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Sanarwan ta ce:

"Iyalan gidan Sanata Afegbua na baƙin cikin tabbatar da mutuwar mace ta farko da ta zama Sanata a Najeriya, Sanata Franca Afegbua."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ta rasu ne da safiyar yau Lahadi, 12 ga watan Maris, 2023. Ta haɗa kyau da basira lokacin da ta bauta wa ƙasa Najeriya (A matsayin mambar majalisar dattawan Najeriya)."
"Nan gaba kaɗan za'a ji bayani game da shirye-shiryen birne marigayyar daga bakin iyalanta."

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa an zabe ta a matsayin Sanata mai wakiltar Bendel ta arewa a watan Oktoba, 1983 karkashin National Party of Nigeria a jamhuriya ta biyu.

Afegbua, mai ahekaru 79 a duniya, yar asalin garin Okpella ce da ke karamar hukumar Etsako ta gabas, wanda yanzu ya rabu cikin jihohin Edo da Delta.

Amma tafiyar siyaaarta ta zo ƙarshe da wuri-wuri lokacin juyin mulkin sojoji a watan Disamba 1983, suka kwace mulki hannun farar hula watanni uku da kafa gwamnati.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Masani ya fadi kura-kurai 5 da CBN ya yi wajen kawo batun sauyin Naira

'Yan Bindiga Sun Halaka Kansila a Jihar Ebonyi

A wani bangaren kuma wasu Miyagun 'yan bindiga sun tare Kansila, sun harbe shi har lahira a jihar Ebonyi

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da Kansilan ke hanyar koma wa gida bayan ya rufe shagonsa da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel