Canjin Kudi: Gwamnoni Ba Su Hakura ba, Za Su Sake Kai Karar Gwamnatin Buhari a Kotu
- Akwai yiwuwar Gwamnoni su sake komawa kotu da Abubakar Malami da kuma Godwin Emefiele
- Lauyan da ya tsayawa wasu Jihohi a shari’ar canjin kudi ya nuna za su iya kai jami’an kotu
- Ana tuhumar Gwamnan CBN da AGF da yi wa kotu kunnen kashi a kan shari’ar canjin kudi
Abuja - Wasu daga cikin gwamnoni sun soma shirye-shiryen shiga kotu da Ministan shari’a, Abubakar Malami da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Rahoto ya zo a Punch a ranar Asabar cewa Gwamnonin za su yi karar AGF da kuma Gwamnan babban banki a kan zargin yi wa kotun koli rashin kunya.
Babban bankin Najeriya na CBN ya ki ba bankuna umarnin su yi biyayya ga hukuncin Alkalan kotun koli na cigaba da kashe tsofaffin N500 da N1000.
Sai a ranar Juma’a ne kotun koli ta gabatarwa gwamnatin tarayya da takardun shari’ar CTC na kotun koli, inda aka haramta soke tsofaffin kudin da aka yi.
Rashin samun takardun shari’ar ya hana tun farko gwamnatin tarayya ta ba Godwin Emefiele damar umartar bankuna su yi biyayya ga babban kotun kasar.
Lauyan Kaduna, Kogi da Zamfara a shari’ar da aka yi, Abdulhakeem Mustapha SAN ya sanar da cewa Abubakar Malami ya samu duk takardun shari’ar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Za a san matakin da za a dauka
Daga yanzu Mustapha (SAN) ya ce za su san matakin da za su dauka idan AGF bai yi abin da ya dace ba.
Idan ba a bi umarnin kotu ba, za mu soma yin shari’a da Babban Lauyan gwamnatin tarayya da Gwamnan CBN.
Idan dai kotun koli tayi magana, ya zama dole duka wakilan gwamnati da kowa da kowa su yi biyayya ga umarninta.
Babu wanda aka kebe, dole kowa ya yi biyayya, shi ne kotun karshe, shiyasa kowa yake da hurumin ikonsa a doka.
- Abdulhakeem Mustapha (SAN)
Lauyan yake cewa jama’a za su ga matakin da za su dauka a kotu idan aka cigaba da yin kunnen kashi, ya na mai nuna za su tuhumi jami’an da sabawa shari’a.
Femi Gbajabiamila zai bar majalisa
Babu mamaki shugaban majalisar wakilan tarayya ya zama shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa idan an rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Rt. Hon. Femi Gbajabiamila yana cikin manya-manyan na hannun daman Tinubu da zai dare mulki, kuma ana ganin ba zai cigaba da shugabantar majalisa ba.
Asali: Legit.ng