Hukumar INEC ta mamayi Shugaban Kasa, an daga zaben Gwamnoni bai da labari
- A yammacin Laraba Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka a garin Daura da nufin zai yi zabe
- Sa’o’i bayan Shugaban kasar ya isa gida sai Hukumar INEC ta bada sanarwar daga zaben Jihohi
- INEC mai zaman kanta ta dauki matsaya ne a daren yau, bayan Buhari ya dawo daga kasar Qatar
Katsina - A ranar Larabar nan ne Mai girma Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya, bayan ya shafe kwanaki hudu ana taro a birnin Doha a Kasar Qatar.
Tribune ta ce Mai magana da yawun bakin shugaban kasa watau Malam Garba Shehu ya sanar da dawowar mai gidan na sa a wani jawabi a jiya.
Shugaban kasar yana durowa Najeriya bai kama hanyar ko ina ba sai mahaifarsa Daura a jihar Katsina, da nufin yin zaben Gwamna da majalisar dokoki.
Muhammadu Buhari ya je kasar Larabawan ne domin halartar wani taro da majalisar dinkin Duniya ta shiryawa kasashen da ke tasowa a Duniya.
Taron majalisar UN a Doha
Shugaba Buhari ya samu damar haduwa da António Guterres wanda shi ne shugaban majalisar dinkin Duniya da kuma wasu takwaransa na kasashen waje.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Leadership ta ce abubuwan da aka tattauna a taron wanda shi ne na biyar sun hada da sauyin yanayi, kalubalen talauci, karancin abinci, da kiwon lafiya.
Masari ya tarbo Buhari a Katsina, sai Daura
Mai girma Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da mukarrabansa suka tarbi tawagar shugaban kasa a babban filin tashi da saukar jirgi na Umaru ‘Yar’adua.
Jirgin Buhari ya sauka garin Katsina ne da kimanin karfe 4:50, daga nan ya wuce gidansa da yake garin Daura a jirgi mai saukar ungulu kamar yadda ya saba.
A nan kuma Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk da ‘yan fadarsa suka yi wa Buhari maraba, da sa ran zai zauna har zuwa bayan an yi zabe.
Garba Shehu a jawabin da ya fitar, ya ce sai an kammala zabe sannan Buhari zai koma garin Abuja da Shugaban kasar ya shafe mako guda kenan bai ofis.
Hukuma ta daga zabe
Babu mamaki abin da shugaban kasar bai sani a lokacin ba shi ne INEC za ta daga zabe, ba zai samu damar kada kuri’arsa ba sai karshen mako mai zuwa.
INEC tana cin gashin kan ta ne, ba ta bukatar yardar shugaban kasa wajen tsaida lokacin zabe, watakila wannan ya hana Buhari tafiya Abuja tun farko.
INEC ta bada uzuri
Ku na da labari cewa Jam’iyyun PDP da LP sun kai kara kan zaben Shugaban kasa, wannan ya jawo aka samu tangarda wajen amfani da BVAS.
Tun da an yi amfani da BVAS a zaben shugaban kasar, wajibi a sake yi masu saiti kafin ayi zaben jihohi, INEC ta ce a dalilin haka aka daga zaben.
Asali: Legit.ng