Manyan Jiga-Jigan PDP da Makusantan Tsohon Gwamna Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Katsina
- Jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar Katsina sun bayyana sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulkin jihar gabanin zaben gwamnoni
- Jam’iyyar ta APC ta bayyana jin dadi da kuma gwarin gwiwar cin zabe a irin wannan lokacin bayan nasarar samun sabbin mambobi
- Ana ci gaba da shirin zaben gwamnoni a Najeriya, a ranar 11 ga watan Maris ne za a yi zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi
Jihar Katsina - Jam’iyyar APC a jihar Katsina ta karbi manyan mambobin jam’iyyar PDP bakwai da magoya bayansu sama da 10,000 a ranar Talata.
Da yawan wadanda suka sauya shekan sun kasance na kusa da tsohon gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Shema, inji rahoton PM News.
Daraktan kamfen APC a jihar Katsina, Mr. Ahmed Musa Dangiwa ne ya bayyanawa manema labarai rahoton yadda jiga-jigan PDP na jihar suka koma APC.
Gwamna ya karbi sabbin mambobin jam'iyyar APC
A cewarsa, gwamna Aminu Masari na jihar ne ya karbi wadannan jiga-jigai zuwa APC gabanin zaben gwamna da ke tafe a karshen makon nan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa:
“Daga cikinsu akwai Alhaji Bashir Tanimu Dutsinma, tsohon mai taimakawa gwamna Shehu, tsohon shugaban karamar hukuma da kuma mamban kwamitin amintattu na zauren Arewa maso Yamma a PDP.”
Ya kara da cewa, sauran jiga-jigan siyasar sun hada da shugabanni da manyan ‘yan kasuwan jihar Katsina, rahoton People's Gazette.
Musa Dangiwa ya kuma bayyana cewa, sauya shekar jiga-jigan na PDP zuwa APC alama ce ta nasara ga zaben gwamna da na ‘yan majalisun jiha a ranar 11 ga watan Maris.
Dan takarar gwamna a jam’iyyar Labour ya janye daga takara a Adamawa
A wani labarin kuma, jam’iyyar APC a jihar Adamawa ta samu karuwa yayin da dan takarar jam’iyyar Labour na gwamna ya sauya sheka, inji rahotanii daga jihar.
Umar Otumba ya ce, ya janye daga takarar gwamna tare da marawa Aisha Ahmed Binani baya a zaben 11 ga watan Maris.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam’iyyar ta APC a Adamawa ke bayyana kaunarta ga kafa gwamnati a zaben nan mai zuwa nan da kwanaki uku.
Asali: Legit.ng