Abin da Emefiele Zai Fuskanta Idan Buhari Ya Sauka a Mulki, Hasashen Shehu Sani

Abin da Emefiele Zai Fuskanta Idan Buhari Ya Sauka a Mulki, Hasashen Shehu Sani

  • Gwamnan CBN za game da tasgaro, ba kuma zai sam mafaka ba idan Buhari ya sauka, ra’ayin sanata Shehu Sani
  • Sanatan ya bayyana hasashensa kan abin da zai faru ne da Godwin Emefiele idan Buhari ya bar mulki a watan Afrilu
  • Idan baku manta ba, Najeriya na ci gaba da fuskantar barazanar karancin sabbin Naira tun bayan sauya fasalin kudin

Najeriya - Tsohon sanata a Najeriya ya yi hasashen abin da zai iya faruwa da gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele zai iya fuskanta idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a mulki.

Shehu Sani ya siffanta halin da gwamnan na CBN zai shiga da cewa, kamar dai Jakin dawa ne a hannun Damisoshi matukar Buhari ya sauka a mulki.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, zababben shugaban kasa Bola Tinubu da wasu gwamnonin Najeriya sun bayyana adawa da yadda aka kawo batun sauyin Naira a kasar.

Kara karanta wannan

Allah ya sa: Buhari ya yiwa 'yan Najeriya alkawari mai zafi, zai cika kafin ya sauka mulki

Shehu Sani ya hango abin da zai faru da gwamnan CBN
Tsohon Sanata Shehu Sani na jihar Kaduna kenan | Hoto: Olubiyo Samuel
Asali: UGC

Idan baku manta bam Legit.ng Hausa ta kawo maku rahotanni a baya na yadda ake kai ruwa rana tsakanin wasu gwamnonin Najeriya da CBN a kotun kolin kasar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A bangaren sauya fasalin Naira, hakan ya kawo kunci da karuwar fatara tsakanin ‘yan Najeriya kasancewar karancin sabbin Naira ya mamaye ko ina a kasar.

Kotun koli ya ce a ci gaba da kashe tsoffin Naira

A wani yanayi mai daukar hankali, kotun kolin Najeriya ya yanke hukuncin cewa, ‘yan kasar za su iya ci gaba da kashe tsoffin N200, N500 da N1000 har zuwa karshen shekarar 2023.

Hakazalika, kotun ya ce dole ne CBN ya ci gaba da karbar wadannan tsoffin kudaden daga hannun ‘yan Najeriya duk kuwa da wa’adin da ya bayar na watan Faburairu.

Da yake karin haske, kotun ya ce umarnin Buhari na sauya kudi ba tare da yin shawari da masu ruwa da tsaki ba bai ma dace ba a tun farko.

Kara karanta wannan

"A Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudi Har Karshen Shekara": Kotun Kolin Najeriya Ta Yanke Hukunci

Emefiele ba zai tsira ba a bayan mulkin Buhari

A bangare guda, Shehu Sani ya bayyana ra’ayin cewa, gwamnan na CBN ya zai samu wata kariya kan wadanda ke sauyin a matsayin barazana ba idan Buhari ya sauka.

A kalamansa, Shehu ya yada a shafinsa na Twitter cewa:

“Lokacin da Baba (Buhari) ya sauka, Emefiele zai dawo kamar Jakin dawa a hannun Damisoshi.”

A wani labarin, bankunan Najeriya sun ce ba za su bi umarnin kotun koli ba har sai CBN ya ce wani abu game da kara wa’adin kashe tsoffin takardun Naira a kasar zuwa karshen shekara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel