Muna Da Kimanin Litan Mai Bilyan 2, Kowa Zai Samu: NNPC Tayi Alkawari

Muna Da Kimanin Litan Mai Bilyan 2, Kowa Zai Samu: NNPC Tayi Alkawari

  • NNPC ya kwantarwa yan Najeriya hankali, yace akwai isasshen man fetur da zai isa Najeriya tsawon kwanaki 42
  • Kamfanin yace daga yanzu zuwa karshen zaben 2023 na gwamnoni kowa zai samu man fetur
  • Sama da watanni hudu kenan yan Najeriya na fama da tsada da karancin man fetur

Abuja - Kamfanin arzikin man Najeriya NNPC ya bayyana cewa yana da isasshen man fetur na lita 1.805 biliyan wanda zai ishe kowa nan da kwanaki 30.

Kamfanin da kansa ya bayyana hakan a hoton bayanin da ya daura a shafinsa na Facebook.

A cewar jawabin:

"Muna da isasshen man fetur a kasa da kuma kan ruwa da isa kowa a fadin kasar nan."
NNPCL
Muna Da Kimanin Litan Mai Bilyan 2, Kowa Zai Samu: NNPC Tayi Alkawari Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: An gano sunayen makiyaya 37 da jirgin sojin sama ya babbaka a jihar Arewa

Hakazalika Kakakin NNPCL, Garbadeen Muhammad, ya bayyana hakan ranar Litinin, 20 ga Febrairu a birnin tarayya Abuja, rahoton Punch.

Ya yi bayanin cewa yanzu haka akwai litan mai miliyan 803.35 a depot yayinda akwai lita bilyan 1 kan jirgin ruwa.

Ya kara da cewa kamfanin ya tanadi yadda za'a samu isasshen man fetur daga yanzu har zuwa karshen watan Maris, 2023.

Yace:

"Muna sa ran samun litan mai milyan 884 kawo ranar 28 ga Febrairu."
"Maris 2023 kuwa, muna sa ran samun lita bilyan 2.3 kuma zai kai 2.5 da zai isa kowa na kwanaki 42."

Sama da watanni hudu kenan yan Najeriya na fama da karanci da tsadar man fetur.

Cikin wannan lokaci kamfanin NNPC ya kara kudin litan man daga N185 zuwa N195.

Duk da hakan mutane basu samun mai a wannan farashi.

A wasu jihohin ma ana sayar da mai har Naira dari uku ga lita.

Kara karanta wannan

"Yanzu Yan Boko Haram Sun Koma Sanya Tufafin Mata Yayin Kai Hare-Hare" - Inji Ndume

Ministan Man Fetur Ya Faɗa Tseren Neman Kujerar Gwamnan Jihar Bayelsa

A wani labarin kuwa, karamin ministan man feturin Najeriya, Timipre Sylva, ya yanki Fom din shiga takarar kujerar gwamnan jihar Bayelsa a zaben da za'a gudanar badi.

Timipre Sylva ya taba mulkin jihar tsawon shekaru hudu karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP.

Ya shiga takun saka da jigogin jam'iyyarsa a lokacin kuma aka hanashi tazarce kan kujerar.

Sylva zai yi takara wannan karon karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel