Yadda Wani Mutum Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce Yayin Dambe Kan Wurin Fakin A Legas

Yadda Wani Mutum Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce Yayin Dambe Kan Wurin Fakin A Legas

  • Wani bawan Allah ya riga mu gidan gaskiya sakamakon rikici da suka yi da wani ma'aikacin kanti kan wurin fakin
  • Rahotanni sun nuna cewa ma'aikacin kantin ya nuna wa direban inda ya kamata ya yi fakin ne amma ya ki, hakan yasa suka fara cacar baki kuma sai dambe
  • Yayin damben ne direban wanda ya taho yi wa mai gidansa siyayya a kantin ya fadi kasa ya dena numfashi, an kai shi asibiti inda likita ya tabbatar ya rasu

Jihar Legas - Wani mutum da ba a riga an gano ko shi wanena ba ya yanke jiki ya fadi ya mutu yayin jayayya kan wurin fakin din mota a wani kanti da ke Admirality Way, Lekki, jihar Legas.

Punch Metro ta gano cewa marigayin, direba, ya tafi kantin ne a ranar Juma'a, 24 ga watan Fabrairu don siyo wa mai gidansa wasu kayayyaki.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben 2023: A Karshe Babban Sarkin Yarbawa Ya Magantu Kan Soke Zabe Da Obasanjo Ya Ce A Yi

Titi a Najeriya
Titin wata unguwa a Najeriya. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma, wani ma'aikaci a kantin ya bukaci a yi fakin din motarsa a wani, shi kuma bai yarda ba.

Wani shaidan gani da ido, Tunji Gafar, ya ce hakan ya janyo jayayya kuma suka kaure da fada.

Gafar ya ce:

"Mutumin ya zo yi wa mai gidansa siyayya kuma kafin ya yi fakin, ma'aikaci a kantin ya nuna masa inda zai yi fakin amma ya ki, ya tafi wani wurin daban ya yi fakin.
"Ma'aikacin ya same shi ya umurci ya gyara fakin, amma ya ki. Hakan yasa suka fara jayaya har aka kaure da fada. Hakan ya janyo hankalin wani cikin shugabanni a kantin.
"Da ya iso, direban ya yanke jiki ya fadi kasa. Da suka gano bai tashi ba, sun fara watsa masa ruwa amma bai farfado ba."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gidan, Sun Harbe Shugaban Jam'iyya Har Lahira

Gafar ya kara da cewa wata mace da suka taho tare da direban ta yi ikirarin cewa ma'aikacin kantin ya buga masa wani abu amma sun musanta hakan.

Ya ce:

"Mun kira tasi mun kai direban asibiti mafi kusa amma suka tura mu wani asibitin. Da muka isa asibitin na biyu aka tabbatar ya rasu."

Martanin yan sanda

Kakakin yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya ce:

"Eh, lamarin ya faru. An tura binciken zuwa sashin binciken manyan laifuka da ke Yaba."

Wani ya yanke jiki ya fadi ya mutu a layin ATM

Wani mutum ya yanke jiki ya fadi ya mutu a harabar wani banki bayan awanni yana jira kan layi a Agbor, jihar Delta.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Fabrarun shekarar 2023 a karamar hukumar Ika South kamar yadda Tribune ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164